Labarai

Hukumar Kwastam Ta Cafke Mota Shake Da Makamai Da Kwayoyi A Owerri

Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya wato, ta yankin “C” dake Owerri na jihar Imo, ta samu nasarar cafke wata babbar mota shake da makamai da mugayen kwayoyi wanda kimar kudinsu ya kai Naira miliyan 9,620,00.

Kayan da aka kama sun hada da, wata babbar bindiga kirar kasar Italiya guda biyu, kakin soja guda 200, harsashi guda 4,375, katan 1,160 na maganin mura na ruwa wato kodin, da katon 300 na kwayar tramol.

Shugaban hukumar na yanki, Mista Kayode Olusemire, ya ce jami’ansu sun samu nasarar cafke wannan haramtattun kayan ne, bayan da suka samu bayanan sirri, an kuma kama mutum uku da ake zargin su ne suka yi safarar wadannan kayan, kuma za a gurfanar da su a babbar kotun jihar dake Owerri a gobe Laraba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button