Kannywood

HOTUNAN MURNAR BIKIN RANAR ‘YANCI SUN JAWO WA FATI WASHA TOFIN ALLA TSINE.

HOTUNAN MURNAR BIKIN RANAR ‘YANCI SUN JAWO WA FATI WASHA TOFIN ALLA TSINE.

Wani sabon salo da jaruman masana’antar finafinai ta kannywood suka shigo da shi a bikin murnar zagayowar  ranar samun ‘yanci na wannan shekarar shi ne suka rinka yada horunan su a soshiyal media sanye da kaya mai alamar  tutar Nigeria. Kusan duk wani fitaccen jarumi da ma wasu da ba  su shahara na sun yi horuna sun tura a dandalin sada zumunci, in da masoyan su suka rinka yin farin ciki tare da taya su murna.

To sai dai a wajen fitacciyar jaruma Fati washa ita lamarin ya zo mata daban ne, domin kuwa yanayin hotunan da ta yi Kuma ta tura su a dandalin sada zumunci ya haifar mata da surutai da kuma tofin Alla tsine daga dumbun masoyan ta in da suka rinka bin ta da zagi da cewar ba ta kyauta ba saboda yanayin shigar da ta yi tamkar tana tallan kanta ne a matsayin wani abu na daban.

Hotunan dai ya nuna yadda ta turo nonuwan ta  da kuma wata yanayin fara’a mai Jan hankalin mai kallo, Duk hotunan da Fati washa ta baza a Dandalin sada zumunci hotuna ne da suke nuna alamar tallata kai ta sigar karuwanci.

Da yawan mutane da suka ga hoton sun sha mamaki da suka ganta cikin shigar da ta yi wani ma abin da ya rubuta a kasan hoton shi ne “Ashe ke cikakkiyar karuwa ce”? Ya yin da wani Kuma ya rubuta cewar ” ko dai ke ‘yar madigoce kike tallan kan ki”? Da sauran maganganu masu zafi da aka rinka yi Mata.

Sai dai wani abu da ya bada mamaki har zuwa yanzu Fati washa ba ta ce komai a kan maganganun da ake yi a kanta ba.

Wannan ta sa wakilin mu ya nemi jin ta bakin ta a game da surutun da ake yi a kan hotunan nata, sai dai mun yi ta kiran wayar ta ba ta daga ba har zuwa lokacin da muka kammala rahoton na mu, amma nan gaba idan mun same ta za Ku ji amsar da ta ba mu.

Me za Ku Ce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button