Labaran siyasa

Haushin faduwa zabe: Tsohon minista ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa

Wani tsohon minista day a fadi zaben zama mamba a majalisar kasa ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa shekaru 20 da suka wuce

Tsohon ministan, Patrick Okumu-Ringa, ya fadi zaben majalisa da aka kamala na kwana-kwanan nan a kasar Uganda. Patrick ya tsaya takarar zama dan majalisa mai wakilta birnin Nebbi ne. Patrick ya mallaki kasa mai fadin gaske a birnin na Nebbi kuma ya gina fanfunan tuka-tuka 10 a wuri daban-daban domin taimakon jama’ar sa.
Tsohon minista Patrick ya bayyana cewar ya cire fanfunan tuka-tukan ne domin jama’ar sa sun yi masa butulci ta hanyar kin bashi kuri’un da zasu bashi nasarar zama dan majalisa. An fara cire fanfunan tuka-tukan ne ranar Litinin, kwana 3 kacal bayan fitar da sakamakon zabe. 
Patrick ne ya zo na 3 da kuri’u 1,270 a zaben da aka kammala. Abokin takararsa Hashim ne ya lashe zaben da adadin kuri’u 4,283 daga cikin jimillar kuri’u 9,940 da aka kada a zaben. 
“Da kudin aljihuna nayi amfani na gina masu fanfon tuka-tuka, yanzu sai gwamnati ta gina masu wasu tunda sun yi min butulci duk da sun san cewar ko gwamnatin kasar Uganda bata samar da ruwa ga jama’a kyauta,” a kalaman Patrick. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button