Hausa Novels

HAUSA NOVEL:Cigaban littafin JENNEFER 3 & 4

Cigaban littafin JENNEFER
3 & 4 Jikinta a sanyaye ta shiga cikin unguwar tana tafe tana hardewa xuciyarta Na bugawa a hnkl har ta karaso gidan wayam taga kofar gidan ta kwankwasa garba me gadi ya bude mata ta shige tana kallon bangaren su yaya khaleel ajiyar xuciyata tayi yau Na tsalleke cin mutuncin yaya haisam kai tsaye dakinta ta nufa ta baje a gadonta tana maida numfashi tunani masu yawa sukai mata cunkus da sauri ta mike ta kunna glof din dakin haske ya kauraye ko ina ta je jikin mudubi ta kurawa kanta ido meyasa bata kama da danginta ? Ta saki ribbon din da ta daure gashinta ya sauka gadan bayanta ta karewa kanta kallo fara ce tasss doguwa bata da jiki tana heart face da dara dara idanu hade da dankaramin baki ta sunkuyar da kanta tabbas kalarta kalan Fulani koma larabawa ne tana da matukar Kyau Sam batayi kama da sauran yan uwanta su David ko mamanta da papanta ba tayi kama dasu koda kuwa ta kafafuwa ko hannaye da yatsu ikon Allah ! Ta girgixa kanta tabbas ikon shine ta danyi tsaki bata son irin wannan tunanin dan yana jefa xuciyar ta cikin rudu da tashin hnkl jikinta asanyaye ta mike ta fice daga dakin tai bangaren hajja kakarsu yaya khaleel kai tsaye ta shige falon ta sameta xaune tana karanta jaridar leadership tayi sallama duk da ba dai dai tayi ta ba hajja ta amsa mata cikin sakin fuska Jennifer naam hajja kin dawo daga wajan Maman taki ko ?? Kanta a sunkuye ta amsa da eh Na dawo hajja tana nan lfy ? Lafiyan ta lau mashaa Allah suka kurawa t.v kallo sbd lbrin da ya ja hankalinsu Na shaye shayen kayan maye da matasa sukeyi hajja taja tsaki Allah ka shirya mana xuri’a amin Jennifer ta fada hade da mikewa kina da wata matsala ne Jennifer ?? A a hajja Na xo Na dubaki ne in da akwai aiki a a babu aiki to zan wuce OK Jennifer gwara kije ki huta ai kina kokari ma sannu ta wuce hajja tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar tana matukar bata tausayi girgixa kai tayi Allah ya shiryeki in dai xaki shiryu  Tana fitowa daga dakin kai tsaye bangaren Rubayya ta shiga ta tana kwance akan gado tana kallon Indian series ( qubul hai ) Rubayya ta dago kai cikin fara’a Jennifer ya akayi ?? Na dawo daga skul ban sameki ba Momy tace min kinje gaishe da Maman David eh cen naje ban dade da dawowa ba ayya ! Kayane gasu nan nayi kwalema nasan xasuyi miki tunda kusan size dinmu daya da murna ta kalli akwatunan data nuna mata wow ! Nagode Anty ruby taxaro ido Anty kuma Jennifer ?? Haba dai dan Allah karki kuma Sa’anni muke fa ngd sosai ruby bako mai kin cancanci fiye da hakan ma ta tashi ta kinkimi akwatin xuciyarta cike da jin dadin kayan ta fice tana mata gdy kai tsaye dakinta ta nufa Taiwa kayan daidaya atamfofine tsala tsala da shaddoji da lesa lesai manya dukkansu kusan sabbine dan babu alamar hudu ko uku ta dafe kai tana murmushi mutanen gidan nan suna da karamci da girmama dan adam duk da bata dade ba dan bata wuce wata 1 da satittika tana musu aiki ba mutun dayane yake masifar gallaxa mata haisam tayi ajiyar xuciya ya tsaneta sbd banbancin addini ta kwanta bacci me karfi ya sureta cike da mafarkai marasa kan gado  7:30 am  Ta tashi ta shiga kitchen ta hau shiryawa yan gidan break fast kasancewar ranar weekend ne har 9:00am bataji motsin kowa ba ta gama ta Jere musu a dinnig ta hau gyra falon ta kade kura ta share ko ina ta kunna turaren wuta ta wuce bangarenta tayi wanka ta dakko kayan da rubby ta bata atamfa brown me adon yellow orange ta saka tayi tayi ta daura Dan kwalin ta kasa haka ta dauko kana nan gyaluluwan da rubby ta hada mata dashi iya wuya tayi rolling din kanta dashi da sauri ta kalli mudubi taja baya a tsorace sak bafulatana ko balarabiya da sauri ta kauda kanta ta dauko break fast dinta ta fara ci hnklinta kwance ta gama ta hau gado ta mike 11:45am ta mike dan taje ta kwashe kayan da suka ci abinci ta kuma Dora lunch ta fito ba kowa a falon ta kwashe ta wanke kayan ta gyara dining area din ta koma kitchen ta hau Dora girki tanayi tana wakarta ta kiristoci tana gyada kai kee !! Cikin tsawa a tsorace ta kame dan tagane muryarsa baki da hnkl ?? Bakisan nan gidan masoya annabi bane kike mana wakar shashanci ?? Ta sunkuyar da kai tana nadamar manta a inda take har tayi wakar ?? Munafuka kafura yaja tsaki me karfi cike da tsana ki dafamin abu me ruwa ruwa yanxun nan sannan idan kika kikai min kazanta ko kisa min wani abun Na cutarwa Allah ya isa ! Wllh I hate u ta runtse idonta don dai bani da yadda xanyi soon xakibar gidan nan kije wajan makiya Allah irinku kiyi musu bautawa gunki fuuuu ya wuce ta tabe baki cike da Jin haushin kalamansa xata jure duk wani cin kashi har lokacin daxata cimma babban burinta da sauri da sauri ta hada masa daga nesa ta hangoshi yana training din daya saba yi kullum ta wuce dakinshi ta ajjiye ta fice da sauri ta cigaba da aikinta ta gama ta shige dakinta tana tunanin bakaken maganganun da haisam ya kwaba mata ….wllh I hate u soon xakibar gidan nan kije wajan makiya Allah irinku ……..ta furxar da huce itakam ba makiyiya Allah bace hawaye ya sauko mata har sai yaushe xata fara kyakykyawar rayuwa Mara tunani barkatai ?? Yaushene xuciyarta xata daina saka mata wasu muhimman abubuwa datake ganin sai ta cinma su xata samu sauki ?? Hayaniya taji me dan karfi na fitowa daga babban falon gidan anyi baki kenan da sauri ta mike dan ita ke kula da baki ta fice tana tafiya a nutse xuciyarta kuma ajagule hayaniyar su haisam da rubby da wasu muryoyi da ba ta sansu ba kai tsaye falon ta shiga hade da sallama suka amsa mata falon cike yake da duk mutanen gidan da ganinsu suna cikin jin dadi dan dukkansu dariya suke bakin fuska biyu ta gani mace budurwa da saurayi dukkansu kyawawa gefe guda ga trolley masu masifar Kyau da gani matafiya ne dan budurwar tayi kama da rubby sannunku da xuwa yauwa yanmata saurayin ya fada yana murmushi hade da kura mata manyan idanuwansa itakam budurwa ta kalleta sama da kasa ta kauda kanta Momy bakuwa mukayi ne ?? Hajja ta ce a a bayan tafiyarka anyi auren zainab wannan itace new maid dinmu ayya meye sunanki yanmata kanta a sunkuye tana murmushi ta amsa da Jennifer.. wat?? Ya fada hade da dan xare ido kina nufin ba bahaushiya bace ?? Eh uban tambaya inji hajja no hajja ba dake nakeba ki rufemin tsohon bakinki mom da mmk haisam yayi tsaki kafura suka kwaso mana dayar macen tace gsky ba tsari ya isa zahra inji rubby kowa yayi me fish sheshi saurayin ya dan girgixa kai sorry Jennifer nyc to meet u ya miko mata hannu ta miko hannu itama da sauri haisam ya bige hannun namijin haba mahboob meye haka ?? Jennifer ta sauke hannunta cike da jin kunya zahra ta kwashe da dariya Momy ta kalleta cikin tausaya wa jennifer jeki jera abinci a dining naga time yayi ga kuma su Zahara da mahboob sun dawo da sauri ta mike ta nufi bangaren kitchen din tana kallon khaleel ko kallon inda take baiyiba asalima danne dannen wayarsa kawai yakeyi tana jiyo hayaniyarsu suna hirarsu cike da annushuwa da jin dadi ta gama jerawa ta karaso Momy gashi cen nagama yawwa jennifer sannu kinji Allah ya saka amin haba mom inji haisam ya kike mata addua bayan kinsan wacece ita haisam .. Haisam.. Haisam mom ya fada tom jikin jennifer a sanyaye xata bar falon taji muryar mahboob Jennifer baxakiyi lunch din damu bane ?? Har abada indai da haisam ne no mahboob nayi nawa tun daxu OK toh shikenan mungode da dawainiya suka hada ido yakashe mata ido daya cikin gwaninta irin salon mayaudaran samari ta juya ta cigaba da tafiya kai kuma taka matsalar kenan itakam bakuwace yanxu take sanin yan gidan wayannan sababbin awajanta ko dame sukaxo ??  

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button