Labaran wasanni

Harry Kane Zai Iya Zama Gwarzo A Laliga -Ramos

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da tawagar kasar Sipaniya, Sergio Ramos, ya bayyana cewa dan wasan gaba na Ingila dan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harru Kane, zai iya zama gwarzo a gasar Laliga idan ya koma. 

Ramos ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai a shirye shiryen da kasashen Ingila da Sipaniya suke yin a buga wasa a tsakaninsu a kasar ta Sipaniya a yau da misalin karfe bakwai na yamma. 

A kwanakin baya dai kasahen biyu sun fafata a junansu inda kasar Sipaniya ce tasamu nasara a wasan daci 2-1 a wasan da aka fafata a filin wasa na Wembley dake babban birnin kasar wato Landan. 

“Harry Kane babban dan wasa ne saboda yanada karfi sannan kuma yanada wayo sosai wanda yakan iya bawa ‘yan wasan baya wahala wajen rikewa sannan kuma yadda yake buga wasa zai iya bugawa a kasar sipaniya” in ji Ramos 

Yaci gaba da cewa “Tabbas banda Harry Kane akwai manyan ‘yan wasa wadanda sai sunyi da gaske sannan zasu iya shawo kansu kuma kasar Ingila ba karamar kasa bace a kwallon kafa kamar yadda kowa yasani”

Harry Kane dai ya zura kwallaye 146 cikin wasanni 223 daya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham sannan kuma shine ya lashe kyautar dan wasan dayafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga gasar cin kofin duniyar da aka kammala a kasar Rasha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button