Labarai

HAJIYA BALARABA TA JAGORANCI SAUKAR KARATUN ALKURANI DOMIN GODIYA GA ALLAH

HAJIYA BALARABA TA JAGORANCI SAUKAR KARATUN ALKURANI DOMIN GODIYA GA ALLAH 
-Yadda Ɗiyar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ta Jagoranci Gudanar Da Saukar Al’ƙur’ani Mai Girma Domin Godewa Allah kan Nasarar da yabawa mai girma Gwamna Baba Ganduje a zangon mulki na biyu.
Hajiya Asiya  Abdullahi Ganduje wacce aka fi sani da (Hajiya Balaraba Ganduje), Basarakiya mai riƙe da sarautar (Fulani Zanan Laisu Fika), ta ɗauki nauyi tare da jagorantar karatun saukar Al’ƙur’ani mai girma wanda yara mahaddata Al’ƙur’ani ƴan ƙasa da shekaru (20) su ka gudanar domin nuna godiya ga Allah kan nasarar da yabawa mai girma Gwamna Baba Ganduje a zangon mulki na biyu.
Da kuma addu’a da tawassuli kan Allah ya ƙarawa Baba Ganduje nasara cikin duk abin da ya sanya a gaba, ya kuma ƙara bayyana masa masoyansa na gaskiya sanna ya kuma kare shi daga dukkan sharrin masu sharri da sharrin maƙiyansa na fili da na ɓoye, ya kuma ba shi nasara da damar gamawa lafiya cikin nasara shi da iyalansa da masoyansa gaba ɗaya. Sannan kuma Allah ya taimaki Jihar Kano ya karo mana zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
Babu shakka Hausawa sun yi gaskiya da su ka ce “Barewa ba ta yin gudu ɗanta ya yi rarrafe”. Duk wanda ya san Baba Ganduje, ya san shi mutum ne mai tarin ilimin addini da na zamani. Kuma shugaba ne nagari wanda ya ke da kishin addinin musulunci gami da yi masa hidima. Duba da yadda ɗiyar mai girma gwamna, Hajiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta ke koyi da ɗabi’un Baba Ganduje wajen riƙo da addini da kuma gudanar da abubuwan ciyar da addinin na musulunci gaba, ko shakka babu ta na matuƙar koyi da mahaifinta.
Sanin kowa ne ya na daga cikin kyawawan halaye da ɗabi’un mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje tara malamai na addinin musulunci su yi saukar Ƙur’ani da gudanar da addu’o’in nemawa Jihar Kano da ma ƙasa gaba ɗaya ƙarin zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a kowane lokaci. Kuma shugaba ne da ya ke martaba Al’ƙur’ani mai girma da kuma karanta shi da yin tawassuli da shi kan dukkan al’amura domin Allah ya biya buƙata.
Ita ma ɗiyarsa Hajiya Balaraba, ba ta wasa wajen koyi da wannan ɗabi’a. A dukkan al’amuranta ta na ƙoƙari da himma wajen gudanar da saukar Al’ƙur’ani mai girma domin neman tabarrukin Ubangiji kamar yadda Baba Ganduje ya ke yi.
Baya ga wannan, Hajiya Balaraba Abdullahi Ganduje, mace ce masaniya mai tarin ilimin addini da na zamani. Ta na kuma da matuƙar riƙo da addini kamar yadda Baba Ganduje ya ke yi. Domin sanin kowa ne, bayan riƙo da addinin har ma ƙarowa addinin magoya baya Baba Ganduje ya ke yi ta hanyar musuluntar da Maguzawa da Kiristoci.
Shakka babu, Hajiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta kai matakin ƙololuwa wajen yin koyi da Baba Ganduje kan yin hidima da tallafawa harkokin addinin Musulunci. Tare kuma da karanta Al’ƙur’ani domin fatan Allah ya shiga lamarinsu ya biya musu buƙatun su na alkhairi, ya kare su daga sharrin masu sharri.
Kuma ko shakka babu, wannan hanya ta riƙo da addini da karatun Al’ƙur’ani da su ka kama ita ce ta taimaka musu Allah ya ke shiga dukkan lamarin nasu ya ke ɗora su a kan maƙiyansu ya ke kuma ƙara haskaka musu masoyansu na gaskiya da kuma munafukai da maƙiyansu. Kuma Babu yadda maƙiya su ka iya dole su gansu su ƙyale domin Allah ya ba su tsaro da ƙariya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button