Uncategorized

Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Gwamna Ganduje Domin “A Tsaftace Nageriya Gaba Ɗaya”.

Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Gwamna Ganduje Domin “A Tsaftace Nageriya Gaba Ɗaya”.

A wani mataki na yaba ƙoƙarin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan kulawa da tsaftar muhalli da kuma sauran shirye-shiryensa kan kula da lafiyar al’umma, gwamnatin tarayya ta gayyace shi domin halartar kamfen mai taken “a tsaftacce Nageriya, ayi amfani da makewayi (banɗakuna) wajen sauke lalura”, wanda za a ƙaddamar a ranar 19 ga wannan wata na Nuwamba mai kamawa cikin wannan shekarar (2019).
Ministan kula da albarkatun ruwa na Nageriya, Mallam Suleiman Hussaini Adamu, shi ne ya bayyana hakan a jiya, a ya yin wata ziyarar neman goyon baya da ya kai wa mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a masauƙinsa na gwamna da ke Asokoro, babban birnin tarayya, Abuja, inda ya gabatar masa da bayanai kan kamfen ɗin na “a tsaftace Nageriya, ana amfani da makewayi”, ma’ana: “Clean Nigeria: Use The Toilet”.
A ya yin jawabin nasa, Ministan ya labarta cewa “a yanzu haka Nageriya na cikin ƙasashe masu yawan al’umma a Nahiyar Afrika waɗanda su ke sauke lalurorinsu a waje a madadin amfani da banɗakuna, sannan kuma a duk Duniya gaba ɗaya ita ce ƙasa ta biyu wacce ta ke da adadin mutanr (Miliyan 47) masu yin tsugunno a filin Allah Ta’ala a madadin banɗakuna.
Sai kuma ya ƙara da cewa “a hankali za mu yi amfani da taswirar tituna domin daƙile wannan matsala nan da shekarar (2025), za mu yi dukkan tsare-tsare da yin duk mai iyuwa wajen tabbatar da cikar wannan buri da mu ka sanya a gaba, mai girma gwamna, hatta wannan ziyara da mu ka kawo maka ta na daga cikin jerin tsare-tsarenmu”. Inji Ministan.
Sai kuma ya ƙara da cewa “Mu na fatan mai girma gwamna zai kasance da mu a ranar ƙaddamar da wannan shiri. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne mu ke sa ran zai ƙaddamar da wannan shiri da kansa, za mu yi farin ciki matuƙa idan mai girma gwamna ya samu damar halarta a wannan lokaci da za a ƙaddamar da wannan shiri a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2019”. Inji Ministan.
A cewar Ministan, za su yi farin ciki idan gwamnatin Jiha ta ƙara ƙaimi kan kula da tsaftar muhalli a Jihar, sannan kuma ya ƙara da cewa, “idan babu kykkyawar nufi a siyasa, kuma aka rasa shugabanni nagari to shirin ba zai yi wani tasiri na azo a gani ba, amma mu na da tabbaci shugabancin siyasa a Jihar Kano ya ba mu tabbacin samun kykkyawar nasara”. Cewar Ministan.
A ya yin da ya ke maida jawabi, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana wannan ƙuduri na tsaftar muhalli a matsayin kykkyawan ƙuduri, “wannan shiri zai samu kykkyawar nasara” inji gwamna Ganduje.
Da ya ke tsokaci game da fatan ganin an sake jan ɗamara sosai kan tsarin tsaftar muhalli, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “domin na ƙarfafa mana gwiwa gaba ɗaya, da kuma fatan ɗorewar kula da tsarin tsaftar muhalli da kula da kiwon lafiyar al’umma, ina mai farin cikin sanar da cewa zan naɗa mai ba ni shawara na musamman kan tsaftar muhalli a Jihar Kano, hakan zai taimaka mana wajen ɗorewar nasara. Inji Gwamna Ganduje.
A wani fata na ganin wannan shiri da sauran shirye-shirye sun yi nasara, gwamna Ganduje ya bayar da shawara cewa “batun ilimantarwa da kuma wayar da kai gami da tursasawa a wasu lokutan su na da matuƙar muhimmanci, tare da waɗannan a muhallanmu, za mu kai matakin nasara kamar sauran ƙasashen Duniya.
“Kamar yadda mu ka kawar da cutar foliyo, kamar yadda ku ka sani shekaru uku baya yanzu mun kawar da cutar foliyo a ƙasarmu, za mu cigaba da yin duk mai yiyiwa domin kawar da dukkan sauran cututtuka a cikin al’ummarmu, za mu tabbatar da cewa muhallanmu sun kasance cikin halin lafiya da tsafta gami kuma da daɗin zama”.
Sannan kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina banɗakunan al’umma da dama domin kawar da matsalar tsugunno a waje, sai kuma ya ƙara da cewa “kuma za mu gayyato hukumomi masu zaman kansu su ma su taka tasu rawar. Wannan ita ce hanya ɗaya tilo ta kulawa da lafiyar muhallanmu”. Inji Gwamna Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button