Labarai

Gwamnatin Tarayya ta fitar da daftarin kasafin kudin shekarar 2019

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da N8.73 tiriliyan a matsayin daftarin kasafin kudin kasa na shekarar 2019. 

Adadin ya nuna cewar an samu ragowar N400 biliyan idan aka kwatanta da kasafin kudin bara da gwamnatin ta gabatar. Sanarwar ta fito ne daga bakin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Sanata Udoma Udo Udoma bayan ya fito daga taron Majlisar Zartarwa na kasa da aka gudanar yau karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa da ke Abuja.

Ya ce majalisar ta kayyade kudin gangan man fetur kan $60, sannan ta na sa ran za a rika samar da gangunan mai 2.3 miliyan a duk rana. Udoma ya ce shirin matsakaicin zango na inganta tattalin arzikin kasa ‘Medium Term Expenditure Framework’ (MTEF) na shekarar 2019 zuwa 2021 ya samu amincewar majalisar kuma nan ba da dadewa ba za a mika shi ga majalisar kasa domin neman amincewarsu. A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewar shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da suka afku a jihar Kaduna sakamakon rikicin da ya barke a Kasuwan Magani na karamar hukumar Kujama da Jihar. Shugaban kasa ya yi kira da al’umma su zauna lafiya da juna kana ya tabbatar da cewa dukkan wadanda aka samu da hannu cikin rikicin za su fuskanci fushin hukuma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button