Labaran DuniyaLabari

GWAMNATIN KANO NA CIGABA DA YAKI DA CUTAR COVID-19- Comrd. Aliyu Garo

GWAMNATIN KANO NA CIGABA DA YAKI DA CUTAR COVID-19-  Comrd. Aliyu Garo

Maigirm Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta jahar Kano, Dr. Kabiru Ibrahim Getso Yace irin Kokarin da Gwamnatin Jahar Kano keyi wajan Yakar Wannan Annoba ta Coronavirus, Ba Kowanne Gwamna Ne ke yiba, Domin Gwamnatin Jahar Kano Na Wannan ai kine da Gaske domin Ganin ta Dakile Wannan Cuta a Fadan Jahar Kano tare da Sauran Cutittika masu Yaduwa.

Cikin Kwarewa da daukar Shawarwari ga Masana Kiwon Lafiya da Gwamnati Keyi Hakan tasa Ake Kara samun Nasarori 100% wajan Yaki da Wannan Annoba ta Coronavirus a Cikin Wannan jahar tamu mai Albarka.

Kadan daga cikin Irin Matakan Gaggawa da Gwamnatin Kano ta Dauke Domin Yaki da Wannan Cuta Sun Hada Feshin Maganin Kashe Kwayoyin Cutittika da Akeyi a Dukkannin Guraren Taruwar Jama’a Dakuma Guraren Ibadu dake Ciki da wajan Jahar Kano.

Haka zalika Gwamnatin Jahar Kano ta Samar da Safar Rufe Fuska masu tarin Yawa Wanda aka Rabasu a Masallatai Kasuwanni da Sauran Gurare Wanda Hakan zai Temaka Wajan Dakile Yaduwar Wannan Cuta a tsakanin jama’a.

Gwamnatin Kano Na Cigaba da Samar da Matakan Ci gaba da Hana Yaduwar Wannan Cuta ta Hanyar bawa Al,umma Shawarwari masu kyau tare da zagayawa Lungu da Sako Domin Yin Gwajin Wannan Cuta Wanda Hakan zai temaka wajan Zagulo masu dauke da Wannan Cuta.

Daga Karshe Getso Yaja Han Kalin Al,umma dasu Cigaba da Kasancewa Cikin tsabta a Koda Yaushe tsabtar jiki data Muhalli Wanda Hakan Na temakawa Wajan Dakile Yaduwar Cutittika.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button