Labarai

Gwamnatin Buhari tana ‘musguna wa ‘yan jarida’

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa gwamnatin Najeriya tana musguna wa ‘yan Najeriya.
A wata sanarwa da kakakin kungiyar Malam Isa Sanusi ya aike wa manema labarai, Amnesty International ta ce gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari tana mamaye ofisoshin buga jaridu sannan ta kulle ‘yan jarida babu gaira babu dalili.
“A shekarat 2018, gwamnatin Najeriya ta tsare akalla ‘yan jarida hudu, alkaluman da suka nunka ‘yan jaridar da aka kama a 2017…kazalika a farkon makon shekarar 2019, jami’an tsaro sun mamaye babban ofishin jaridar Daily Trust da ke Abuja da kuma ofishinta da ke Maiduguri, inda ta kama ‘yan jairda biyu da kuma kwace kwamfutoci da wayoyin salula,” in ji sanarwar, wacce ta ambato shugabar kungiyar Amnesty International Nigeria, Mrs Osai Ojigho.
Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta kara da cewa ‘yan jarida na fuskantar karin hatsari a Najeriya saboda suna wallafa makaloli da kuma neman ganin hukumomi sun yi aikin da ya rataya a wuyansu.
“A shekarar 2018, an daure ‘yan jarida Tony Ezimakor na jaridar Daily Independent, Musa Abdullahi Kirishi na Daily Trust, Samuel Ogundipe na Premium Times da kuma Olanrewaju Lawal na Daily Sun were saboda kawai sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata”.
Kungiyoyi da dama dai na kokawa kan karuwar take hakkin ‘yan jarida a Najeriya, ko da yake gwamnati ta sha zarginsu da rashin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button