Labarai

Gwamnan PDP da bai ji dadin nasarar Atiku ba ya yi wuf ya fita daga wurin taro

Duk da an sanar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin mutumin da ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, har yanzu taro bai kare ba.

Amma abin mamaki sai ga shi mai masaukin baki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi wuf ya fice daga filin taron.
Wike ya fice ne bayan ya gaisa a gur-guje da Atiku domin yi masa murna. Da ficewar gwamnan magoya bayansa suka dunguma suka bi bayansa.
Gwamna Wike na sahun gaba a cikin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar PDP dake goyon bayan takarar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto babu wanda daga cikin Wike ko Tambuwal ya yi magana a akan sakamakon zaben.

Atiku ya samu kuri’u 1,532 da suka ba shi nasara a kan Tambuwal, da ya zo na biyu da kuri’u 693 da kuma ragowar ‘yan takara 10.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button