Labaran siyasa

Gwamnan Neja ya samu form din takarar 2019 a sama

Jama’a sun sayawa Gwamnan Sani Bello fam din takaran 2019

Mun samu labari cewa Maza da Mata na ‘Yan kasuwan Jihar Neja sun sayawa Gwamnan Jihar watau Abubakar Sani Bello fam din tsayawa takara a zaben 2019 domin ya zarce kan kujerar sa. 


An sayawa Gwamnan Neja fam din takaran 2019 domin ya zarce Source: Twitter 

Manyan ‘Yan kasuwan Jihar Neja daga Kananan Hukumomi 25 na Jihar su ka fanshi fam din takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a madadin Gwamna Abubakar Sani Bello domin ya sake takara a zabe mai zuwa a APC. ‘Yan kasuwan Jihar wanda Shugaban su watau Yusuf Moshe ya jagoranta sun sayi fam din ne a babbar Hedikwatar Jam’iyyar APC da ke babban Birnin Tarayya Abuja. Gwamnan dai yanzu ya huta da kashe Miliyan 22 wajen fam din takara. ‘Yan kasuwan sun yaba da irin rawar da Sani Bello yake takawa a matsayin sa na Gwamnan Jihar kamar yadda Ahmad Salihu wanda ke magana da bakin Kungiyar ya bayyanawa ‘Yan Jarida. ‘Yan kasuwan sun ce Gwamnam yana yi da su. 

Daga cikin alheran da Gwamnan yayi wa ‘Yan kasuwar kamar yadda su ka fada shi ne sama masu wutan lantarki. Kungiyar ta dai nuna takaicin ta wajen shan gaban ta da aka yi na sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam da aka yi a makon jiya. 

Source: naij.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button