Labarai

Gwamnan Jihar kano Yagabatar da Naira Billion 219 a matsayin kasafin kudi na shekarar 2019.

A jiya ne Laraba 14 ga Watan Nuwamba, 2018, Mai Girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019, ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya yi wa lakabi da Kasafin Kudin Samar Da Cigaba Mai Dorewa.

Kasafin kudin na tsabar kudi Naira Bilyan Dari Biyu da Sha Tara (N219B), an ware Naira Bilyan Dari da Talatin da Hudu da Milyan Dari Shida (N134.6B) a matsayin na manyan ayyuka. Sai kuma ayyukan yau da kullum an ware musu Naira Bilyan Tamanin da Biyar (N85B).

Bangaren gine-ginen ayyukan cigaban kasa su ne suke dauke da mafi tsokar kasafin kudin, da a ka ware musu Naira Bilyan Talatin da Takwas (N38B). Bangaren albarkatun ruwa kuma an ware musu Naira Bilyan Ashirin da Shida (N26B). Yayin da harkar lafiya a ka ware Naira Bilyan Ashirin da Biyar (N25B), wanda ya dau kashi sha biyar cikin dari na gaba dayan kasafin kudin.

Harkar Ilmi kuma an ware mata Naira Bilyan Goma Sha Takwas (N18B). Yayin da bangaren Noma kuma a ka ware masa Naira Bilyan Tara da Milyan Dari Hudu (N9.4B). Bangaren muhalli kuma an ware masa Naira Bilyan Uku (N3B). Yayin da a ka ware Naira Bilyan Biyu da Milyan Dari Takwas (N2.8) ga bangaren Tsaro.

Daga cikin manyan ayyukan da suke kunshe a wannan kasafin kudi, da a ka kudiri aniyar yi a wannan shekara ta 2019 mai shigowa sun hadar da yin wata sabuwar gadar sama  wacce za ta taso tun daga Kofar Mata ta bi ta kasuwar Singer daga nan kuma sai ta hade da titin Murtala Muhammad Way.

Za a fadada titin Katsina road da kuma titin Malam Aminu Kano Way. Za a yi, da Iznin Allah, Mayankar dabbobi ta zamani. Sai kuma rukunin gidaje guda dari masu daki dai-dai da kuma gidaje guda dari masu daki biyu-biyu, masu saukin kudi.

A bangaren ilimi kuma za a kara samar da sababbin ajujuwa guda 1,000. Da kuma samar da kujeru da teburan karatu ga ajujuwan da mu ke da su. Za a kashe kudi har Naira Bilyan Shida (N6B), a ayyukan da za a yi a manyan makaratun jihar. Wadannan ayyuka da za a yi sun hadar da gyaran dakunan karatu da sauran muhimman abubuwa da su ka shafi harkar karatun a wadannan wurare.

Saboda bukatar inganta samar da cigaban al’umma tun daga tushe, an ware kudi har kimanin Naira Bilyan Biyar (N5B), saboda yin amfani da su ga dukkanin mazabu guda 484 na kananan hukumomi 44 da ke wannan jiha. Kowace mazaba za a kashe mata Naira Milyan Goma (N10M).

Saboda dalilin bude sabon shafi a komawa ta biyu da Iznin Allah, ga wannan gwamnati ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sa za a bayar da wata kulawa ta musamman ganin an kammala ragowar ayyukan da wannan gwamnati ta gada kafin karewar zangon farko. Wannan kuma duk a na yi ne saboda a kara tabbatar da cigaba da mulkin dimukuradiyya ke haifarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button