Labaran Duniya

GWAMNA GANDUJE YA GANA DA SHUGABANNIN ƘANANAN HUKUMOMI NA JIHAR KANO

GWAMNA GANDUJE YA GANA DA SHUGABANNIN ƘANANAN HUKUMOMI NA JIHAR KANO
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi murna kan nasarar da aka samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna a Jihar Kano inda jam’iyyar (PDP) da ɗan takararta Abba Kabir Yusuf su ka shigar da ƙara su na ƙalubalantar nasarar da ya samu shi da jam’iyyarsa ta (APC) a babban zaɓen shekarar (2019) da ya gabata.
A ya yin da ya ke yaba musu game da rawar da su ka taka a lokacin zaɓen, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “akwai buƙatar na taya ku murnar wannan nasara da mu ka samu”.
A saboda kun fahimci cewa, idan ya kasance cewa, a matsayinku na shugabannin ƙananan hukumomi ku na da bambancin jam’iyya da gwamna, tafiyar ba za ta yi daɗi ba. Alhamdulillah waɗannan nasarori da mu ka samu a rumfunan zaɓe da kuma kotu ya zama lallai mu taya ku murna”. Inji gwamna Ganduje.
Gwamna Ganduje ya gabatar da waɗannan jawabai ne a ya yin da ya karɓi baƙuncin wakilan shugabannin ƙananan hukumomi ƙarƙashin ƙungiyarsu ta (ALGON) reshen Jihar Kano bisa jagorancin mataimakin shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar Bunkure Onarabul Rabi’u Bala inda su ka ziyarce shi a masauƙinsa na gwamna da ke Asokoro babban birnin tarayya Abuja domin taya shi murnar wannan nasara da ya samu a kotu.
Inda kuma daga nan ne mai girma gwamna ya ba su tabbacin gwamnatinsa na cigaba da yin aiki tare da su kafaɗa da kafaɗa domin cigaba da samar da cigaba a ƙananan hukumominsu da ma Jiha gaba ɗaya, inda ya ƙara musu ƙwarin gwiwa da cewa: “ku kasance masu kusanci da kykkyawar dangantaka da al’umma a ƙananan hukumominku, a kowane lokaci ku zamto masu himma da ƙoƙarin fahimtar al’ummominku domin cigaba da kyautata rayuwarsu”. Inji gwamna Ganduje.
Sannan kuma, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin da su cigaba da kulawa da taron tattauna sha’anin tsaro da muhimmanci gami kuma da dubansa a matsayin haƙƙi, kuma wani nauyi da ya rataya a wuyansu. Tare da ƙarawa da cewa, tsaro na daga cikin jerin abubuwa mafiya muhimmanci a rayuwar al’umma. Inda ya tuna musu cewa, “a mafi yawan lokuta al’umma ba sa yabawa sha’anin tsaro har sai ya zama mai armashi”. Cewar gwamna Ganduje.
Daga nan kuma sai mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yaba musu kan irin rawar da su ke takawa cikin shirin ciyar da ɗalibai a makarantu. Inda gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin wani fanni na ciyarwar ita ma gwamnatin Jiha da ta ƙananan hukumomi su ka ɗauki wani fannin, “ya zama wajibi na yaba muku kan wannan rawa da ku ke takawa”. Gwamna Ganduje ya bayyana.
Bayan da ya kammala ba su umarnin cigaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya a dukkan masarautun Jihar, gwamna Ganduje ya nanata aniyarsa ta ganin ya tabbatar da haƙiƙanin cigaba a sauran sabbin masarautu (4) da ya samar a Jihar.
Kuma a wannan ƙoƙari nasa na samar da cigaba a sabbin masarautun, yanzu haka ana daf da fara aikin samar da manyan asibitoci waɗanda za su ci gadajen kwantar da marasa lafiya a ƙalla guda (400) domin kyautata sha’anin kula da kiwon lafiya a dukkan masarautun huɗu.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin, (ALGON) ta Jihar Kano, Onarabul Bala, ya taya mai girma gwamna murna tare da ba shi tabbacinsu na cigaba da marawa gwamnatin baya wajen ciyar da Jihar gaba.
Kamar yadda ya ke cewa: “Ƙudurinmu shi ne bin tafarkin mahaifinmu, mai girma gwamnanmu, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Ranka ya daɗe, mun zo nan ne domin taya ka murna gami da ba ka tabbacin cigaba da samun haɗin kai da goyon bayanmu”. Inji shugaban (ALGON) na Jihar Kano.
“Za a iya tunawa mun haɗu a cikin sha’ani daban-daban tun bayan yanke hukuncin kotu, amma wannan dama ce ta musamman da mu ka samu mu ka zo a jimlace cikin ƙungiya domin taya mai girma gwamna murna kan wannan nasara da ya samu”. Cewar Shugaban ƙungiyar ta (ALGON).
Daga ƙarshe kuma, dukkanninsu sun godewa mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da irin goyon baya da haɗin kan da ya ke ba su wajen tafikar da ƙananan hukumominsu cikin nasara da aminci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button