KIMIYALabaraiLabaran Duniya

GWAMANTIN JIHAR KANO TA BADA UMARNI DA A BUDE GIDAJEN KALLON BALL NA FADIN JIHAR

GWAMANTIN JIHAR KANO TA BADA UMARNI DA A BUDE GIDAJEN KALLON BALL NA FADIN JIHAR

 Mai Girma Gwamna, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR yayi taro na Musamman da Shugabannin masu gidajen kallo da cinema na Jihar Kano wanda Gwamnatin Jihar Kano tabasu damar su bude gidajen kallonsu daga gobe don fara kallon gasar Laliga ta Kasar Spain wanda yin hakan ze kara dawo da tattalin arzikin Jihar Kano.
Gwamna yace duba da yadda matasa suke da shaawar kwallon kafa yasa za’a bude wadannan gidaje daga bisani an hore su dasu kasance masu bin dokokin Gwamnati da Jami’an Lafiya, sannan Gwamnati tabasu safar rufe hanci domin rabawa mutane masu shiga kallon don kaucewa cutar Coronavirus.

Gwamna yana tare da Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Sakataren Gwamnati Alh Usman Alhaji, Kwamishinan Yada Labarai Mal Muhammad Garba da na Muhalli Dr Kabiru Ibrahim Getso da Sakataren Hukumar Tantance Fina finai Mal Ismail Naabba Afakalla.Yau,Juma’a. 12/6/2020

Abubakar Aminu Ibrahim
SSA Social Media, Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button