Labarai

GWAGWARMAYAR JANYO TEKU ZUWA AREWA……..
Sabuwar tashar jirgun ruwa da shugaba muhammad buhari ya bude 


Marigayi tsohon Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua shi ya fara bada aikin tashar Jiragen Ruwa ta Baro tare da cire makudan kudade domin aiwatar da aikin. Sai dai aikin ya gamu tafiyar hawainiya a lokacin da Shugaban ya fara jinya.

Bayan rasuwar Shugaban kasa Yar’adua, Shugaban kasa Jonathan ya umurci ma’aikatar kudi ta maido da kudaden aikin tashar Jiragen Ruwa wadanda suka kai Naira Biliyon 19 zuwa asusun ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta domin yin wani muhimmin aiki a yankin na Neja-Delta. Daga wannan lokaci murnar da yan Arewa keyi na samun babbar tashar Jiragen Ruwa na farko a jihar Neja ya koma ciki.

ANFANIN TASHAR JIRGIN RUWA GA YANKIN AREWA.

> Tashar tana karamar hukumar Agaie dake jihar Neja…

> Tashar zata samarda guraben ayyuka da suka kai Miliyon Biyu.

> Sanadiyar tashar, manyan jiragen Ruwa masu dauko manyan kaya zasu fara shigowa Arewacin Najeriya.

> Dan Arewa zai samu saukin jigilar kayan da ya sayo daga kasashen waje.

> Zamu huta da zuwa Tashar Jiragen Ruwa dake kudanci domin karbar kayan da muka sayo a kasashen ketare.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanun da tashar Jiragen Ruwa ta Baro zata kawowa yankin Arewacin Najeriya. Wannan na cikin namijin kokarin da shugaba Buhari yayiwa yankin Arewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button