Labarai

GIDAUNIYAR GANDUJE TA MUSULUNTAR DA MAGUZAWA 200..


A yammacin  Juma’ar data gabata ne aka musuluntar da maguzawa a Kimanin su 200 dasuka fito daga Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano Karkashin Gidauniyar Ganduje Foundation wadda ke Karkashin Jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam.

 A Jawabinsa,Gwamna ya bayyana Godiyarsa ga Allah bisa damar daya bashi yake Gabatar da wannan aikin kusan Shekara 23 dasuka wuce wanda yahada da Gina Masallatai,Makarantun Islamiyya,Aikin Ido,Musuluntar da maguzawa dasauran aikace aikacen Gidauniyarsa,Sannan ya bayyana aniyar kawo karshen Maguzawa a duk inda suke a Jihar Kano.


Taron wanda Yasamu Halartar Gwamnan Kano nada Mal Ibrahim Shekarau da Manyan Malamai 
daga sassa daban daban irinsu,Shugaban Kungiyar Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakatarensa Sheikh Kabiru Abdullahi Gombe,Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa,Wakilan Shugaban Darikar Qadiriyya Karkashin Sheikh Jabiru Sheikh Nasiru Kabara,Wakilan Tijjaniyya Karkashin Sheikh Mal Yusif Ali Gabari,Shugaban Izala Na Jihar Kano Sheikh Abdullahi Sale Pakistan da sauran Malaman Jihar Kano duk a Karkashin Kulawar Mai Bawa Gwamna Shawara akan Harkokin Addinai Alh Alibaba Agama Lafiya Fagge.

A Jawabinsu Kowannensu ya Godewa Gwamna bisa Wannan Kokari da Gidauniyarsa takeyi tare da yimasa Fatan samun Nasara a Duniya da Lahira insha Allah daga bisani Gwamna ya Jagoranci rabawa Kowace mace Atamfa da Naira dubu 10 Maza Kuma shadda da Naira dubu 10 domin su kama Sana’a.

ALLAH YASAKAWA GWAMNA DR ABDULLAHI UMAR GANDUJE DA ALHERI.

Source: Abubakar Aminu Ibrahim
SSA Social Media II,Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button