Abin Alajabi

Gaskiyar Lamarin: Yadda Mijina Ya Mutu, Maryam Sanda Ta Sanar Da Kotu

Gaskiyar Lamarin: Yadda Mijina Ya Mutu, Maryam Sanda Ta Sanar Da Kotu


A jiya ne babban kotun tarayya dake Maitam ta cigaba da sauraron shari’ar Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta kuma uban ‘yarta.

Cikin zubda hawaye ta sanar da alkalin kotun cewa bata taba fatan mijinta ya mutu ba balle kumaita da kanta ta halakasa.

Maryam, ta bayyana cewa fasassar kwalbar Shisha da ta tarwatse yayin da suke rigima da mijin nata ne ta sokesa a kirji Maryam Sanda da ake zargi da hallaka mijinta Bilyaminu Bello, ta fadi hakikanin abinda ya ja mutuwar mijinta a gaban babban kotun tarayya da ke Maitama, Abuja.

A jiya ne aka cigaba da sauraron shari’arsu.

Sanda ta sanar da kotu yayin da take zubda hawaye cewa, duk da akawai matsaloli a auren nata na shekaru biyu, amma ba ita ta kasha mijinta ba.

 Ta sanar da kotun cewa, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017, ta yi amfani da wayar maigidan nata don yin kira amma bayan nan sai ta ga hoton tsiraicin wata mata a wayar.

Ta je wajensa don bukatar Karin bayani, amma sai rigima ta sarke tsakaninsu wacce ta kaisu har dare. Ta bayyana cewa, ta bukaci saki amma sai marigayin ya shaketa.

Ta shiga daukan caja dinat amma sai ya tureta har ta fadi kasa. Hakan kuwa yasa ta ture kwalbar Shisha dinsa har ta fashe. “Ya danneni a kasa sai muka ji kukan ‘yarmu.

Na rokeshi akan zanje in ga me takewa kuka shine ya sassauta min riko.

Yayin da nayi kokarin tashi ne shi kuma ya fadi inda fasassar kwalbar ta sokeshi a kirji,” cewar Sanda.

 “Na cire masa kwalbar sannan na kira wani Ayuba inda ya taimaka min na kaisa asibiti inda aka ce min ya rasu.

Ban aminta ba, hakan yasa na kara kaishi babban asibitin Maitama inda nan ma aka tabbatar min da ya mutu.” fadin Sanda.

 “Daga asibitin ne aka kaini ofishin ‘yan sanda inda na rubuta abinda ya faru. Ban kashe mijina ba. Ban taba fatan yamutu ba,” in ji Sanda.

Ta sanar da kotun cewa, a lokacin da ta nufi asibiti da mijin nata, fasassar kwalbar Shisha din da ruwanta suna nan a falonsu.

 Alkalin kotun, Jastis Yusuf Halliru y adage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba inda za a yanke hukunci.

Idan kuna da Bukatar Bamu Labarin Abunda Ke Faruwa A Jihar Ka, Yankinka, Anguwanka Ko Turo Mana Ra’ayin ku ko bukatar bamu Shawara, tuntube mu a: Hausafinest1@gmail.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button