Labarai

Ganduje yayi kwangen biyan miliyan 2.9 a karar da ya kai Daily Nigerian

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi kwangen Naira miliyan biyu da dubu dari tara a karar da yakai Jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar inda yake neman a biyashi diyyar Naira biliyan uku.
Babbar kotun jiha karkashin mai Shariah Namallam a ranar 19 ta dakatar da jaridar Daily Nigerian daga cigaba da wallafa faifan bidiyon Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a shafin jaridar na intanet.
Sai dai kuma babban lauyan dake wakiltar Jaafar Jaafar da Daily Nigerian MB Danazumi ya nemi kotun da ta yi watsi da Wannan shariah duba da yadda Gwamnan yayi kwangen Naira miliyan 2.9 na kudaden shigar da karar.
Danazumi ya bayyana cewar takardun bayanai na kotun sun nuna cewar Sai wanda yake kara ya biya wadannan kudade kafin gurfanar da wanda yake kara, inda yace, Gwamnan bai biya kudin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button