Labarai

Ganduje yasha alwashin kawo zaman lafiya a yayin zabe mai zuwa

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake ya gayyaci sauran abokan takararsa dake takarar kujerar gwamnan jahar zuwa fadar gwamnati domin tattaunawa akan yadda za’a samar da dawwamammen zaman lafiya a kafin da bayan zaben 2019.
Majiyar ta ruwaito Ganduje ya bayyana haka ne a jiya Laraba, 24 ga watan Janairu a yayin taron rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya daya gudana a jahar Kano, wanda sauran yan takara 28 suka samu halarta.

Kungiyar zaman lafiya a yayin zabe ta jahar Kano ce ta shirya wannan taro daya gudana a jami’ar Bayero ta Kano, a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, tsohon shugaban kasa Abdul Salam Abubakar da wakilin majalisar dinkin duniya, Muhammad Ibn Chambas.
A jawabinsa, Ganduje yace a matsayinsa na gwamnan jahar Kano, wajibi ne a gareshi ya tabbatar da ganin an samu zaman lafiya a yayin zaben 2019 da kuma bayansa, don haka yace yana gayyatar sauran yan takara zuwa fadar gwamnatin jahar Kano domin tattauna yadda zasu tabbatar da zaman lafiya a Kano.

“Na yi farin ciki da wannan taron zaman lafiya, wannan shine abinda na sa a gaba a matsayina na gwamna, babban jami’in tsaro na jahar Kano kuma shugaban jam’iyyarmu, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin zabe da bayan zabe.
“Shi yasa nake kokarin tabbatar da dimukradiyya a cikin gidan jam’iyyarmu, kokarin tabbatar da yan jam’iyya sun girmama juna, tare da girmama abokan hamayya, wannan ne yasa bamu yarda magoya bayanmu su dauki makami zuwa yakin neman zabe ba.” Inji shi.
Shima a nasa jawabin, mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II ya ja hankalin yan siyasa game da tafka magudin zabe, inda yace zaman lafiya ba zai samu ba muddin yan siyasa basu daina daukan siyasa tamkar ‘A mutu ko ayi rai ba’.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button