Labaran siyasa

Ganduje ya mayar da fam dinsa na takara, yace yana tare da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya mayar da fam dinsa na ra’ayin takarar kujerar gwamna a zaben 2019 sakatariyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ne ya karfi fam din daga hannun gwamnan. Ya samu rakiyan Sanata Barau Jibrin, tsohon ministan ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, yan majalisar dokoki masu ci da sauran yan takaran da suka mayar da fam dinsu. 

Ganduje wanda ya ba shugaban jam’iyyar na kasa tabbacin cewa mutanen Kano na tare da shi da Shugaba Buhari, yace sun dauki tsarin zaben fidda gwani na kato-bayan-kato domin ba duk mambobin jam’iyyar damar zabar shugabanninsu.

A halin da ake ciki, wani jigon jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Alhaji Hashim Ubale Yusuf ya bayyana cewa zai yi takarar kujeran gwamna domin ya gyara barnar da gwamnan jihar mai ci, Muhammad Abubakar Badaru ya haddasa.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis, 3 ga watan Satumba a jihaar Kano, Yussuf yayi zargin cewa gwamnan jihar Jigawa ya dauki wata hanya ta daban daga wacce kundin tsarin mulkin APC ke kai.

Yayi ikirarin cewa gwamnatin Badaru a Jigawa ta gaza a yankunan noma, lafiya, ilimi da kuma tsaro.

Source: naij.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button