Labarai

Ganduje ya gabatar Wa Majalsar Dokoki kasafin Kudin Naira Biliyan 197.68

Ganduje ya gabatar Wa Majalsar Dokoki kasafin Kudin Naira Biliyan 197.68
Daga Saifullahi koki 
A yau Alhamis ne Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya
gabatar wa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2020 na
Naira Biliyan 197.68 don neman amincewarsu.
Gwamna Ganduje ya yi wa kasafin kudin lakabi da ‘Budget of Sustainable
Social Development’ ya kuma ce, kasafin zai mayar da hankali ne wajen
bunkasa jihar.
Ya ce, an ware Naira Biliyan 117.71 don fustkantar manyan ayuyuka
yayin da kuma aka ware Naira Biliyan 79.972 don yin ayyukan yau da
kullum.
Daga nan ya ce, kasafin kudin wannan shekarar bai kai na shekarar 2019
ba, a shekarar 2019 an ware wa  ayyukan yau da kullum Naira Biliyan
219 wanda haka ke nuna kashi 16 16 ne na abin da aka ware a wannna
shekarar.
Gwaman ya kuma bayyana cewa ana sa ran samun kudaden da za a kashe a
kasafin kudin ne ta harajin da za a tattaro a cikin gida wanda ake sa
ran samun Naira Biliyan 40 da kuma kudaden da za su shigo assun jihar
na Naira Biliyan 143.9 wanda Naira Biliyan 70 za su fito daga asusun
gwamnatin tarayya.
Ya kuma ce, an ware kaso mafi tsoka ga sashen ilimi wanda ya samu
naira Biliyan 49.9 billion, hakan kuma na nuna cewa, sashin ilimin ya
samu kashi 25.23 na kasafin kudin ne gaba daya.
Haka kuma sashin ayyuka zai samu Naira Biliyan 33.8,  Harkar samar da
kiwon lafiya kuma ya samu Naira Biliyan 30.7 yayin ayyuka na musaman
ya samu Naira Biliyan 33.7 sai aikin gona wanda ya samu Naira Biliyan
5.4 sai harkar shari’a ya samu Naira Biliyan 7.9 yayin da muhalli ya
samu Naira 3.3.
Bayanin ya kuma nuna cewa, an ware wa harkar samar da ruwan sha Naira
Biliyan 15 sai bangaren sifiri ya samu Naira Biliyan 5.9, raya karkara
kuma ya samu Naira Biliyan 3.4 sai kuma bangaren tsare tsare ya samu
Naira Biliyan 3.6 sai bangare yawon bude ido da al’adu ya samu Naira
Biliyan 382.34 yayin da aka ware wa bangaren harkar adini Naira
Biliyan 646.81 a shekara mai zuwa.
A jawbinsa,Shugaban majalisar, Alhaji Abdulazeez Garba-Gafasa ya ce,
yan majalisar za su gaggauta tataunawa tare da amincewa da kasafin
kudin ba tare da bata lokaci ba.
Ya kuma yi alkawarin cigaba da aiki da bangaren zartaswa kafada
da kafada don cigaban jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button