Labaran siyasaLabari da dumi-dumi

Ganduje ya bayyana dalilin da yasa ya tsige rawanin Sunusi Lamido Sunusi

Ganduje ya bayyana dalilin da yasa ya tsige rawanin Sunusi Lamido Sunusi

Gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce, Muhammad Sanusi, tsohon Sarkin na Kano, ya rasa kujerar sa saboda ya ki ya kasance wani bangare na sake fasalin tsarin masarautu.

Gwamnan ya kirkiro masarautu guda hudu a kokarin su na inganta tsaro da sauran nau’o’in cigaba, anyi wannan matakin ne cikin tsari da dacewa wajen gudanarwa.

Hukumar Kula da Laifin Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta zargi Sanusi da almubazzaranci da kudaden da kuma gabatar da bincike a kansa.

Sanusi ya hau kan karagar mulki ne a ranar 8 ga Yuni, 2014, bayan mutuwar Ado Bayero, wanda ya yi sarauta daga 1963 har zuwa rasuwarsa a 2014.

Da yake magana a wani taron manema labarai don nuna bikin ranar dimokiradiyya a ranar Litinin, Ganduje ya ce garambawul din da ya yi “sun tabbata”.

Gwamnan ya ce “Tsohon Sarkin na Kano, wanda bai yarda ya zama wani bangare na sauye-sauyen ba, a haka dai har ta tabbata Masarautu sun kafu kuma sun zauna daram,” in ji Gwamnan.

“A yau, babu batun shari’a a gaban kotu dangane da kalubalan tar sake fasalin tsarin masarautun gargajiya.”

Ganduje ya ce shawarar da tsohon sarkin da wasu dattawan suka yi na kalubalantar “sake fasalin” sa a kotu ya kawo tsaiko ga matakin, kuma hukumomi a Kano za su ci gaba da bincike shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button