Kannywood

Ga jerin jaruman kannywood da suka fice cikin shekara 2016Akwai jarumai da suka fice cikin 2016 sanadiyar yanayin yawan fitowar su da kuma yadda fina-finai da suka fito ya samu karbuwa a wajen masoyan fina-finan hausa na masana’antar kannywood. Wajen fitar da wannan jerin sunayen dandalin finai-finai na Pulse ta hada gwiwa tare da masu sharhi da kuma masoyan fina-finan kannywood. Ga jerin jarumai 10 da suka fice cikin shekara 2016;

Adam A.Zango Fina-fina wanda ta shahara da wannan jarumin ya fito cikin 2016 “basaja gidan yari” da “afra”
Ado Gwanja wannan jarumin ya shahara wajen fitowa a wasan barkwanci kuma shahara wajen raira waka.

Aisha Aliyu Tsamiya Jaruma Aisha wanda ta fara fitowa cikin shirin fina-finai cikin shekara 2012 ta samu suna yayin da fito cikin shiri “So” wanda tayi da Adam A.Zango da kuma “Dakin amarya”. Cikin fina-finai da fito cikin bara sun hada da “Yar mama”, “ Salama”.

Ali Nuhu Wanda aka yi wa lakabi na “sarkin Kannywood” dan wasan kwaikwayi ne, mai shiryawa kuma mai bada umarni ne na masana’antar fina-finan hausa. Ya fito cikin shirin “Kasata”, “indon kauye”, “Kisan hutu”.

Fati Shu’uma Fatima Abubakar wanda aka fi sani da Fati Shu’uma, yar shekara 23 ce wanda ta fara shahara a cikin masana’antar. Ta fito cikin shirin; “Basma”, “Yar mallam”, “Yan Gambia”.

Jamila Nagudu Jamila wanda ake wa ikirari na “gimbiyar kannywood” bara fito a shirin fim da dama. Ta fito cikin shirin “Mahauciya”, “Kaddara ko son zuciya” “Maula”.
Rahama Sadau Rahama Sadau ta shigo masana’angtar cikin 2013 kuma ta shahara bayan fitowar ta cikin shirin “Gani ga wane” tare da tauraron kannywood Ali Nuhu.
Ta fito cikin shirin; “Ana wata ga wata”, “ Hallacci”. Sadiq Sani Sadiq Wannan jarumin ya fara shirya fina-finai kana ya koma ga fitowa da kansa a shirin fim. Ya fito a cikin “kasata”, “Iyalina”.
Suleiman Bosho Ya fiye fitowa cikin wasannin barkwanci. Ya fito cikin shirin “Headmaster”.

Nuhu Abdullahi Shima Nuhu Abdullahi ya fara shirya fina-finai kana ya koma ga fitowa cikin shirin fim. Ku kasance tare da domin bayanar da fitattu na bana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button