Labaran siyasa

Fitaccen tsohon dan Wasan Najeriya ya Sadaukar da Gidansa don kamfen din Buhari

Tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya, Daniel Owefin Amokachi, ya sadaukar da wani babban gidansa dake kan titin Raba a garin Kaduna domin yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben shekarar 2019. Bayan sadaukar da gidan nasa, Amokachi, ya dauki alkawarin bayar da gudunmawa iya karfinsa wajen yiwa Buhari kamfen domin ya cigaba da zama shugaban kasar Najeriya har zuwa shekarar 2023. 

An haifi Amokachi ne a watan Disamba na shekarar 1972 a garin Kaduna. 

Amokachi na da tagwayen yara; Nazim Amokachi da Kalim, wadanda ya ce burinsa shine ya ga sun bugawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasan kwallo. 

Bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa, Amokachi ya zama mataimakin mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya a shekarar 2007 da kuma tsakanin shekarar 2008 zuwa 2014 kafin daga bisani ya zama mai horar wa na wucin gadi daga shekarar 2014 zuwa 2015. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button