KIMIYA

Fasahar matasa: Wani matashi ya kirkiri injin dake maida tarkacen ledoji zuwa fetur a Najeriya (Hotuna)

Fasahar matasa: Wani matashi ya kirkiri injin dake maida tarkacen ledoji zuwa fetur a Najeriya (Hotuna)

Wani matashi a Najeriya mai tarin fasaha mai suna Emeka Nelson ya samu fikirar kera wani injin mai ban mamakin gaske da zai taimakawa muhalli da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya idan har aka kara bashi kwarin gwuiwa.
Fasahar matasa: Wani matashi ya kirkiri injin dake maida tarkacen ledoji zuwa fetur a Najeriya (Hotuna)

Matashin dai Emeka yace injin din da ya kera yana markadewa tare da tace tarkacen bola kamar su ledoji da kuma robobi inda kuma yake sarrafa su ya zuwa man fetur domin anfanin al’umma.

MAJIYARMU ta samu cewa matashin dai ya saka hotunan injin din ne a shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Facebook wanda har yanzu yana cigaba da jan hankalin al’ummar kasar musamman ma matasa.

Fasahar matasa: Wani matashi ya kirkiri injin dake maida tarkacen ledoji zuwa fetur a Najeriya (Hotuna)
Haka zalika matashin ya kara da cewa da fasahar kirkirerren injin din tasa wadda ya sawa suna Mgbanwe C12 zai iya mayar da tarkacen na bola ya ziwa man gas na manyan motoci da kalanzir dama kwanon rufin gidaje ko buloluwan zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button