Labari da dumi-dumi

EFCC TAYI BABBAN KAMU; EFCC Ta cika Hannu da Isma’il Mustapha A.K.A Mompha

EFCC TAYI BABBAN KAMU; EFCC Ta cika Hannu da Isma’il Mustapha A.K.A Mompha

Wakilinmu Yahaya Muhammad, Abuja

Hukumar yaki da almundahana da Dukiyar kasa wanda aka fi sani da EFCC tayi ram da Shahararren Dan danfarar nan na kafafen sada Zumunta wanda ake kira da Isma’il Muhammad wanda aka fi saninsa da Mompha wanda ya shahara wajen damfara da fasa kaurin Kudin mutane a yanar gizo

Isma’il ya fada komar Jami’an tsaro sun

kama shi ne ranar Juma’ar data gabata 18 ga wata a babban filin jirgin sama na Abuja a shirinsa na samfewa zuwa kasar Dubai biyo bayan bayanan da aka samu a Kan sa.

A rahoton da hukumar EFCC ta fitar ta bayyana cewar yazo yana shirin fitane daga kasar cikin hanzari, hakan ya tilasta ma hukumar yin gamayyar hadin gwuiwa domin tabbatar da ya shiga Hannu don gudanar da bincike a kansa amma Ismail ya shaida cewar yana aiki ne a karkashin ofishin hukumar canjin Kudi.

Bincike ya tabbatar da cewar shi wanda ake Zargi wato Ismail yana  amfani ne da  Harkallar BDC.

Haka kuma wanda ake zargin ya bayar da dukkan bayanai na irin abubuwan da ya gudanar a muhallin sa na basira .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button