Labaran siyasa

EFCC ta fara binciken Abdullahi Baffa Bichi


Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin azrikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kaddamar da bincike akan zarge zargen cin hanci da rashawa da ake zargin korarren sakataren gidauniyar makarantun gaba da sakandari, TETFund, Dakta Abdullahi Baffa Bichi.

EFCC ta kaddamar da binciken ne bayan ta samu takardun korafe korafe daga wata kungiya mai zaman kanta dake rajin yaki da rashawa a ma’aikatun gwamnati, Center for Public Accountability, CPA.

Babban sakataren CPA, Olufemi Lawson ne ya rattafa hannu kan takardar korafin da kungiyar ya aika ma EFCC inda take tuhumar Baffa da laifuka da suka shafi danganci rashawa, bayar da kwangila ba bisa ka’ida ba, wulakanta ofishinsa da kuma karya dokokin hukumar.
Sai dai Baffa ya musanta wadannan zarge zarge, amma duk da haka ana sa ran EFCC za ta gayyaci Baffa da kungiyar CPA a kokarinta na tabbatar da sahihancin tuhume tuhumen ko akasin haka.

Shugaban CPA, Lawson yace sun mika korafe korafensu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da kuma Ministan sharia kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami.
Kungiyar ta zargi Baffa da umartar jami’o’in gwamnati dasu ware kashi 20 na kudaden ayyukan kwangiloli da hukumar Tetfund ke yi a cikinsu domin amfanin masu ruwa da tsaki, sai dai hukumar tace tana da tabbacin babu wani masu ruwa da tsakin da suka wuce Baffa, iyalansa da abokansa.
Haka zalika CPA ta zargi Baffa da yin amfani da yan uwansa da abokansa wajen samun kwangila daga hukumar Tetfund, a manyan makarantu daban daban dake fadin kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button