Kannywood

Duba hotunan jaruma Rahama Sadau na motsa jiki da su ka gigita maza

Wasu hotunan jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, na motsa jiki da jaridar Legit.ng ta ci karo da su a dandalin sada zumunta ta yanar gizo, sun sa haifar da cece-kuce da cacar baki a tsakanin maza.
A yayin da wasu mazan ke nuna jin dadinsu daganin yadda jarumar ke motsa jiki domin kulawa da lafiyar jikinta, wasu sun bayyana mabanbancin ra’ayi.
Samun maza, musamman matasa, na yin tsokaci a kan fitattun mutane, musamman jaruman fim da mawaka, ba bakon abu ba ne.

Wasu daga cikin masu bayyana ra’ayinsu a kan hotunan sun nuna matukar soyayyar su gare ta, har ta ki ga wasu na rokon ta daure ta aure su.

Wani daga cikin irin maza cewa ya yi, “da kyau Rahama Sadau, motsa jiki abu ne mai kyau, kuma matukar mace na son dadewa ba ta tsofe ba, dole ta rungumi motsa jiki. kin yi daidai.

Babu wani cikakken bayani a kan yaushe ne jarumar ta dauki hotunan ko kuma wurin da aka dauke su ba, illa dai an ga jarumar sanye da makaran kunne da ke kai sauti tana motsa jikinta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button