Tarihi

DOLE MU FADAWA DUNIYA ALHERIN KWANKWASO- DALIBI WANDA AKA DAU NAUYINSA KARATU- A.B SAGAGI

I HAVE REASON TO DECIDE ONE OF THEM

MU FADAWA DUNIYA ALHERIN SA (kukan kurciya)

By: S.koki
11-10-2018

Bayan na gama makarantar gaba da sakandare na samu guraben karatu da dama dan ci gaba da karatuna na gaba da sakandare, na shiga makarantu akalla sun kai uku a cikin birnin jihar kano, wandanda suka haka da kano state college of art and remedial studies (C.A.S) sannan aminu kano college of legal studies (legal kano) daga karshe na samu damar shiga maitama sule university ,kano wadda aka sani a baya da northwest university kano, duk wadannan makarantun dana lissafo ban samu damar kammalawa ba , kasancewar ba abin da nakeso na karanta bane nake samun gurbin karatun sa a wadannna makarantun, makaranta ta karshe dana shiga a jerin makarantun dana lissafo itace northwest university kano, inda suka bani gurbin a tsangayar koyo da sarrafa harkar kasuwanci, wato bussines administratioin. A wanna lokaci na hakura na sa a raina zan zauna nayi abin da ya kamata duk da ba abin da nake son karanta bane suka bani amma saboda kada na cika gaba da bata lokaci. Haka na hakura na fara wannan karatu, ina ta kokari ina zuwa makaranta a sannu a hankali kuma ina gane duk abinda ake koyawa a aji.

Wata rana sai amini na yazo ya sameni bayan na dawo daga makaranta a gajiya, yake sheda mun cewa, gwamnati mai ci a wannan lokaci fa tana so zata debi yan asalin wannna jiha tamu zuwa makarantu masu zaman kansu na cikin wannan kasa daban daban, nayi murna da jin hakan kuma na dauki hakan kamar a matsayin wata dama ce tazo min. Bayan kwana biyu sai yazo ya sake cemin am fara kai takardu ministry of higher education gwamnati nan ba da dadewa ba zata tura karatu kamar yadda ya shaida min a baya, haka dai kamar zamu kai kamar bazamu kai ba, haka muka tattara takardun mu na shaidar gama sakantare da takkardar jamb da mukayi a wannan shekara muka kai ministry, dukm da haka bamu sa rai ba, musamman ma ni dayake a takardar jarabawa ta ta kammala sakandare ban samu lissafi ba wato mathematics, kuma ance sai wanda yake da 9 credit sannan kuma yaci jamb, haka dai muka kai wannan takardu namu, a lokacin aka hadamu da wani bawan allah da yake aiki na ministry of higher education a wannan loakci, saboda ya taimaka mana , ranar farko da muka je muka sameshi ya fada mana magan ganu marasa dadi, a lokacin sai da takai ta kawo har mun fara cire rai sakamakon irin abubuwan daya farfada mana.

Haka dai muka ci gaba da addua, muka ki mu fidda rai, kullun muna jewa wataran a kasa wataran kuma in mun samu kudi sai mu hau abun hawa daga unguwannin mu muzo ministry mu duba ko an kafe sunaye. Bayan an dauki kusan satu uku duk sati sai munzo ministry a kalla sau hudu, wani sati da ya zagayo bamuje ba, kwatsam wannan aboki nawa yana dawowa gida ya samemu yake fada mana an kafe sunaye a ministry shima yana dawowa ne daga makaranta yake gani, dan a lokacin shima yana kan karatun sa na diploma a kano state polytecnic (matan fada), haka muka dunguma dukan mu a lokacin mu shida ne yan unguwar mu wanda muka nemi wannan scholarship na gwamnati cikin ikon allah dukkanin mu munga sunayen mu, amma cikin ikon allah wannan aminin nawa baiga sunan sa ba. A lokacin sai suka ce za,a sake kafe wasu sunayen dan hak duk wanda naiga suann sa ba kar ya damu, bayan sati daya aka kikiramu wadanda aka kafe sunan mu domin screening da interview. Muka lallaba su 5 dinnan da aka kafe sunayen mu muka zo aka mana screening kowa aka karbi takardun sa akaga wane department ya dace a bashi gurbin karatu a wannan lokaci, akace kowa ya tafi ya saurara, za’a sake kafe sabon sunaye wanda kowa zai ga abin da ya dace ya karanta a jami’ar da gwamnati zata kaishi.

Haka muka zauna zaman sauraro, duk wannan abin da ake yi, ban fadawa kowa a gida cewa na samu gurbin karatu a wata makaranta da gwamnati ce zata dauki nauyin mu ba, saboda nasan halin mahaifina, a wannan lokacin sai nai yunkurin na fada a gida amma in ta kokonto a cikin raina, haka dai na daure na fada a gida kamar yadda nake tunani hakan ce ta faru, ina fadawa mahifina sai yace shi baya goyon bayan na tafi saboda yasan halin gwamnati watakila muje akaimu karatu , daga baya kum gwamnati tazo ta zare hannun ta, saboda hakan ya faru sau da yawa a tsarin scholarship da gwamnati take dauka, nayi iyaka kokarin cewa a barnui na tafi amma ina abin yaci tira. Hakan nan ba yanda zanyi nai ta bakin ciki, da abin nake kwana araina kuma dashi nake tashi, saboda zanso ace mun tafi tare da sauran abokaina mu 5 a ganina karatun zaifi mana dadi tinda dama ko a gida kullun muna tare tamkar wasu yan uwa jini daya.

Ana cikin wannan hali ne, sai aka sake kafe sunaye da ranar da gwamnati zata dauki mutane ta kaisu wannan makaranta mu wadanda mukayi screening kenan anan naga an bani admission akan naje na karanci nazari kan halayyar dan adam da abinda ke kewaye dashi (Sociology) dama abinda da nake ta mafarkin na karanta kenan tin a fari bayan kammala sakandare dina k, suma sauran abokan nawa kowa yaga nashi abinn da zai karanta biyu daga ciki zasu karanta bangaren accounting sauran biyun kuma saya chemistry daya kum political science, a wannan lokaci naji araina ina mutukar kaunar na tafin wannan makaranta a wannan tsari n gwamnati, to amm ga abin da mahaifina kuma ya fada min, anan nayi ta shawarwari daga karshe na yanke shawarar cewa naje na sami mahaifiyata na sake mata bayani ki za’a samu a lallabashi ya barni na tafi, haka kuwa akayi naje na sameta na mata cikakken bayani, tace to insha allah in ya dawo zataje ta sameshi ta msa bayani. Haka ko a kayi a wannan satin wannan gwamnati ta wannan lokacin ta hada gagarumin taro a gidan gwamnati, gwamna ya fito yayai bayani, sannan yja gargadi mu kan cewa kowa ya tsaya yaje yayi abin da ya kaishi, yayi mana nasiha sosai tamkar yayan da ya haifa a cikin sa daga karshe gwamna yayi mana raha dama akwaishi da barkwanci, inda yake cewa in ban manta ba ” idan uka kaiku karatu ku tsaya su maida hankali , kada labari yazo mana cewa anga wani yan tafiya da reverse” bayan an kammala taro sai akayi sanarwa cewa duk wanda aka kafe sunan sa to yaje ministry oh higher education ya jira za’a zo a abashi shaidar samun gurbin karatu wato admission letter sannan kuma mutun zaiga makarantar da aka kaishi,haka kuwa akayi bayan an kammala muka wuce ministry, muka zauna zuwa dan wani lokaci sai ga wani jami’in gwamnati nan a wannan lokaci, shi yazo ya rarraba mana wannan takardu anan naga amakarantar da gwamnati zata kaimu wata jami’ar musulunci ce mai zaman kanta a jihar katsina. Haka na koma gida ina murna, na nunuwa mahaifiyata, sannan mahaifina na dawowa shima naje na nuna masa shima.To a cikin wannan sati dama gwamnati ta yanke shawarar cewa cewa a cikin ranakun hutun mako mai zuwa kowa ya shirya, kayan ka kawai ake bukatar ka dauko zuwa ministry, gwamnati zata kawo motoci kowa akaishi makaranta da kuma wurin da zai dinga kwana. A cikin wanna sati ana ta lallaba mahaifina cewa ya barni n tafi amma ina har saida takai ta kawo satin da ranar tafiya ta zagayo, da naga haka har na fidda arai, in ajira abokaina kwai naji ance sun tafi dan ko fita daga gida na kasayi, kwatsam sai daya daga cikin abokanan namu yazo yace min ai an daga tafiyar mu sai sati mai zuwa saboda gwamnati na so da kammala wasu yan shirye shirye da ba’a kammala ba wanda ya shafi wurin kwanan mu da zamu zauna da sauransu, nayi murna dajin wannan zance matuka.nan fa na dukufa da yin addua ba dare ba rana, saboda har ga allah ina so na tafi saboda an bani abin da nake ta mafarki na karanta.

Bayan sati ya zagayo saura kwana daya a tafi, sai na sake zuwa nacewa mahaifina gobene gwamnati zata turamu makarantar data dauki nauyin mu kamar dayya aka shaida masa a baya, bayan na fada sai nai shiru ina jiran naji yana nan akan qadamin sa ko yaya, cikin iko allah sai yace to naje na dauki kayana set 4 idan naje na fada masa yadda yanayin makarantar yake da inda aka ajiye mu, amma sati daya zanyi na dawo, dajin haka ban musa ba kuwa nje na fara shirya kayana, na hada kayana tsaf jira nake kawai gari ya waye mu wuce ministry dan ranar ma na kasa bacci an zumudi.gari na wayewa na dauki jakata dam karfe 7 akace kowa ya fito naje na samu abokaina wadanda zamu tafi tare dasu, aranar nayi murna amma murna mai hade da bakin ciki, abin da ya jawo min bakin ciki shine, amini na da muka nema tare amma shi bai samu ba. Kuma mun san haka ba rashin cancanta bace ba, kawai dai wani al’amari ne daga ubangiji, haka aka kawo motoci kusan guda goma dan mun ada yawa sosai a kalla mun kai kusan 450.haka muka rabu da abokanan da suka mana rakiya muna ta kewar juna.

BAYAN AN KAIMU KATSINA

Bayan kaimu katsina kowa na ta raba idanuwa yaga shin ina za’a kaimu can sai muka ga kowa an rarraba su ma’ana hakan yan nuna kowa an tafi dasu makwancin su. Muma muna cikin mota sai muka ga anyi wani wuri damu daban, zuwa wani lokaci sai driver din mu yayi parking a gaban wani saban gida, gidan gidan benene da alamar kuma ba’a dade da kammala gininsa ba, nan akace to kowa ya sakko ya dauki kayan sa, muka sauko aka bude boot muka daddauki kayan mu, dam mu 5 dinnna mun atre bamu rabu ba, sai kuwa aka bude gida kowa ya shiga da kayan sa kowa kuma ya samu daki, kamar yadda al’adar kowa take in y shiga sabon gida abu 2 ake dubawa ruwa da wuta ai kuwa wasu daga cikin mu sai aka kunna famfo aka ga ruwa yazo dam wuta tun kafn mu shiga gidan muka hangi wuta a ciki. Anan fa aka hau ihu ana kara abinku da dalibai saban yanka in ban manta ba waka muke ana cewa “ga ruwa ga wuta” dan muna da yawa da aka zubamu a wannna gida akalla mun kai mun kusa 100 ko wane daki mutun 4, kuma manyan dakuna ga fanka ga manyan bandakuna a wadace, a takaice de gida yayi ga sababbin katifu da aka kawo mana washegari dan ranar da mukazo a kan tsofaffi muka kwana kafin a kawo sababbi. Wannan gida in ba karya zanyi ba ko inda nake kwana a gidan ubana bazai nuna masa komai ba. Byan mun huta muka kira gida muka shaida musu irin lafiyayyen gidan da aka sauke mu kuma ga ruwa ga wuta ga bandakuna masu kyau, in fact sai kace gidan sabuwar amarya na fadawa mahaifiyata da muke waya. Bayan na kammala sai na kira mahaifi na nake shaida masa inda aka kaimu wuri ne me kyau nan dai baice komai ba, sai shardi da ya bai cewa, in na shiga makaranta naje a canja min course din da aka bani zuwa wani daban wanda yakeso ni nayi, bance komai ba nace to,

Bayan mun huta ranar lahadi, Monday sai kowa ya shiga makaranta anan ne kowa ya fita daga hayyacin sa, saboda alokacin munje katsina ana wata azababbiyar rana mai sa mutun ya fita daga hayyacin sa, dan wannan rana ta kori mutane da yawa da mukazo dasu wanda sai wasu aka kawo a madadin su. Duk da haka nayi ta kokari naga nabi duk wata hanya da za’a canja min course kamar yadda mahaifina ya umarce ni amma ina, yayi ta kirana yana hadani da mutane da yasani suke aiki a makarnatar kan cewar naje na samesu a canja min course amma ina abin bai yuwu ba, bayan na kwana hudu a kwan na 5 biyar din ranar juma,a sai naga kiran mahaifina a waya yace dam ya kirani ne ya fadamin cewar ya yanke shawara na zauna naci gaba da karatuna bama sai na canja course ba da jin hakan nayi murna matuka kwarai da gaske akarshe yamin nasiha da addua yace allah ya bada sa’a kuma muyi karatu sosai, ranar kwana nayi ina farin ciki.

Haka muka ci gaba da rayuwa mu 5 dukda bayan wani dan lokaci muma an samu daya daga cikin mu da ya gudu yace wahala tayi yawa shi bazai iya zaman garin ba, nan muka rage saura mu hudu, karatu na ta tafiya har takai an kusa fara jarabawa, akazo akayi jarabawa ta zangon kartu na farko bayan an kammala, makaranta tace babu hutu kowa ya dawo sati me zuwa za’a cigaba da karatu a sabon zango. Haka muka hakura muka zauna da muna ta doki da zumudin zamuje gida hutu, a wannan lokacin sai da mukayi kusan wata 5 bamuje gida hutu ba sai da aka kare zangon karatu na 2 sanna akayi hutu muka koma gida.

Bayan hutu ya kare mun dawo sai gwamna ya turo wakilan sa cewa a shaida mana yaji ance wasu na gudowa cewa, duk wata gwamnati ta dauki nauyin zata bawa kowa naira dubu ₦10,000 ga duk dalibin da ya zauna yaci gaba da karatu, sannan kuma nan bada dadewa ba kowa gwamna zai saya masa na’urar kwamputa dan saukaka wasu wahalhalun karatun, saboda makarantar da aka kaimu, makaranta ce wadda sai dan wane da wane ne suke iya karatu a cikin ta, dan ko kudin makaranta da ake biya akalla a lokacin yafi karfin dubu ₦150.000, haka kuwa akayi bawan mun cika wata tara a wannan makaranta, gwamna ya turo wakilai cewa kowa a dauki sunansa da sauran bayanai za’a biya naira dubu 90,000 kamar yadda yayi alkawari, sannan kuma a shaida mana cewa nan bada jimawa ba zaizo ya kawo mana ziyara, wannan zancen ziyarar yafi zancen kudin dadi, saboda ace yau gwamna zai taso takanas ta kano ya zo dan ya ganka ai ba karamin abu bane. Haka kuwa akayi bawan wasu kwananki kowa aka tura masa ₦ 90,000 a account ba dadewa kuma kowa aka kawo masa computer sababbi a kwalin su aka raba wadda a lokacin darajarta takai naira ₦190,000. Kowa ya karbi kwamfuta akayi ta murna, sauran daliban makaranta suka ta kishi dam suna cewa an kawo musu yan kauye yayan talakawa zasu bata musu makaranta, da dai sauran magan ganu na yayan masu hannu da shuni marasa da’a, ganin wannan abunda gwamna yayi mana a wannan lokaci yasa , muka kara kima a idan daliban makarantar.

Rayuwa na ci gaba da tafiya, duk bayan yan watanni gwamna sai ya biya mu kudaden da ya mana alqawari. Bayan an kammmala ajin farko na jami’a, hakika mutanen mu da dama sunyi kokari kuma an kammala aji daya da sakamako mai kyau, dan was daga cikin mu ma sune jagorori a department din su. Ana ta tafiya karatu na kara yin gaba ayi hutu a dawo, hat takai ta kawo, wani lokaci zai zo da damu taba tinanin abubuwa zasu canja ba ta fuskar gwamnati, kuma hakan ya faru ne bayan tenure din mai girma gwamna ta kare, bayan anyi zabe sabon gwanna yazo, wanda a farko muna tinanin zaici gaba d daukar dawainiyar mu, kamar yadda gwamnan daya gabata yayi dawainiya damu, ashe abubuwa zasu canja.

A lokacin da gwamnati takaimu karatu, dama ashe aqa’ida ne gwamnati bata biyan kudin makaranta baki daya sai dai a abiya na wani lokaci daga baya aci gaba da biya a hankali a hankali, to a lokacin wancan me girma gwaman na farko, ya biuya mana kudin karatun da zamu kai har aji 2, shi kuma saban gwamna da yazo sai yakewa makaranta barazanar cewa bazai karasa biyan kudin makaranta ba, wanda yadinga sawa wadan su lokuta sai makaranta tace bazata barmu mu rubuta jarabawa ba, sai an shiga an fita sai kaga allah yasa makaranta ta kyalemu mun rubuta jarabawa, a haka akai ta tafiya makaranta na mana barazana in lokacin jarabawa yazo, har takai mun kai aji hudu wanda shine ajin mu na karshe a wannan jami’a. Wani abun mamaki shine wannan saban gwamna, tinda ya karbi ragamar mulki, yake allah wadai da kaimu ma karatun da akayi ti a farko, acewarsa wai ba akan tsari aka kaimu ba, alhalin yana daga cikin jami’an gwamnati na waccan tsohuwar gwamnati shima, kuma na tabbata inda akwai dansa a ciki bazai taba fadar haka ba, bugu da kari, wannan kudi na 10,000 da tsohon gwamna yake bamu, tinda saban gwamna ya hau ko kwandala bai taba bayarwa ba.
Ana cikin wanan yanayi yakai yanayi gashi a wannan lokaci, an shiga matsalar tattalin arziki a kasarmu, dan abin da za’a baka a gida bazai isheka ba, tinda mu ba yayan wasu bane gaba dayan mu ko dan kansila babu a cikin mu, hakan tasa dalibai da dama aka shiga wani hali, karatun ma yafara gagara sai mai karfin hali shine zai iya karatu yadda ya kamata. Wannan dalili yasa wadansu daga ciki dayawa suka samu matsala, saboda wasu daga cikin mu kafin tahowar mu suna dan kasuwancin su, an san dai dam mutumin Kano ba’a rasa shi da kasuwanci ba. Tom jin cewar gwamnati tad au nauyi kuma an fara wannan karatu har ana bawa kowa 10,000 dun wata yasa wasu daga ciki kasuwan cin ma suka ajeshi a gefe, dam kuma karatun nasu sukewa kasuwan ci kafin gwamnati ta dauki nauyin su, wannan yasa daliban mu da yawa suka shiga cikin wani hali marasa dadi musamman wajen results da sauran su.

An ta wanna rayuwa ne har Allah ya kawo mu shekara ta karshe a wannan makaranta, a lokacin makaranta na sake mana barazana cewar fa bazata bar mu muyi jarabawa ba, saboda tinda tsohon gwamna ya biya kudin makarantar mu na aji 2, haryau gwamnati bata sake basu komai ba, hankalin dalibai ya tashi , yasa aka dinga tinanin hanyoyin da za’a bullowa da wannan al’amari, a haka dai wasu suka daga cikin shuwagaban nin mu na SPONSOR STUDENTS samu dama suka dawo kano, suka bi duk matakan daya dace dan ganin gwamnati ta biya makaranta ko da kadan ne na daga cikn kudaden da suke binta. Amma duk da haka abu yaci tira, said a takai ta kawo har wasun mu sun fara shiga gidajen radio dake birnin jihar Kano, sannan aka samu gwamnati ta fara Magana Akan batun kudin makarantar da ake binta. A haka dai aka lallaba ahar mukayi jarabawar karshe t agama jami’a duk da haka hankalin dalibai bai gama kwanciya ba, saboda kowa na tinanin ko an kamala karatu makaranta, bazata bada shedar kamala karatun degree din mu na farko ba, hakan yasa shuwagaban nin mu sukai tabi daga wannan hanya zuwa wannan hanya har zuwa lokacin da aka gama kamala karatu kowa duk wanda y agama anyi shagali anyi murna yan uwa suka dinga tasowa takanas ta kano har zuwa katsina dan taya mu murna, aka gama bikin gama makaranta kowa ya waste. Bayan wata 1 da yan kwanaki sai wata maganar ta sake fitowa cewa, makaranta t ace bazafa ta bawa kowa shaidar kamala makaranta ba, matsawar gwamnati bat agama biyanta kudaden da take binta fa, nan fa hankalin kowa ya kasa kwanciya dan wusu ma bacci basa iyawa.Kowa Yana tsoron kar duk shekarun da mukayi da karatun da mukayi anyishi a banza. Dan an samu nasarori da yawa, dan wsu daga cikin mu da yawa sun lashe kyaututtuka daban daban saboda hazakar da suka nuna a karatun su, dan a takaice duk wani department dake makarantar da ake ji dashi acikin uku da suka fi kowa kokari sai ka samu biyu ko daya daga cikin GOVERNMENT SPONSOR students, wanda hakan ya kara samarwa da jihar mu kima da kwarjini a idan duniya.
Ana kan wannan Magana ne ta matakin da makaranta zata dauka in har gwamnati bata kammala biyanta kudin da take binta ba, sai shuwagan nin mu sukayi shawara cewa a inda ake hawa tan an ake sauka. Ma’ana su koma gun wancan tsohon gwamnan duk da bashi bane ba Akan mulki amma yana da alfarmar da a kasar mu ba abin da zai nema a ko ina ne a fadin kasar ba’a masa ba. Hakan kuwa shine ya faru, suka bi duk wata hanya daya dace dan ganin kukan mu ya koma wa tsohon gwamna, cikin ikon Allah kuwa sai zance ya koma masa, anan ba ayi wata wata bay a tintibi makarantar dan jin me yake faruwa, anan suka shaida masa komai. Akarshe dai maganar da yayi dasu ita tasanya har Allah yasa duk wanda ya kammala bashi da matsala, ya karbi takardar shedar kammala karatun sa a hannu, dan kawowa yanzu da yawa daga cikin mu muna cikin wata na bakwai a bautar kasa wato NYSC a sassa na kasar nan daban daban.

Wani kuma abin takaici ban haushi da tausayin shine game da maganar sauran yan’uwan mu da suka samu matsala a baya cikin karatun su, Wanda takai har sai sunyi abinda ake cewa SPILL OVER, to ita dai spill over dama dayan biyu ce akwai ta sakaci sannan kuma akwai ta qadara kuma ko wacce tazo ba yadda za’ai ka kauce mata, sai dai ace Allah ya sake rufa asiri kuma ya kiyaye gaba, abinda yake faruwa kawowa yanzu shine, wadanda suka rage a makaranta suna gyara anji labarin cewa gwamnati tace bazata biya musu kudin da suka zauna yin gyara ba saboda sakacin su yasa hakan ta faru a kansu, wanda ahakan da dama daga cikin su ba sakaci bane, kawai yanayin  rayuwa ne daya sauya saboda munga yanayin kwazon da sukayi a farkon fara karatun mu, wasu kuma dama qaddara ce ba yadda zasuyi. Shiyasa nake so nayi amfani da wannan dama ta karfin social network kan cewa dan ALLAH duk wanda yasan yana da ruwa da tsaki a wannan al’amari dan Allah ya taimaka a roki saban gwamna daya taimaka ya karsa biya musu. Akwai takaici ace kayi shekara 5 kan karatun degree amma a karshe bayan ka kammala ashe baka da wata shaida ta kammala wani karatu.  Abin da takaici kuma zai jefa wasu daga cikin su a mawuyacin hali.

Allah ya sakawa tsohon gwamna da Alkhairi
ENG. DR RABI’U MUSA KWANKWASO.

Dalili shine;
1. Ya dauke mu ya kaimu makarantu munyi karatu har matakin degree alhalin mu ba yayan kowa bane.
2. Ya Samar mana da muhallin da muka zauna mukayi karatu cikin jin dadi har karshen tenure dinsa, wanda wasu daga cikin mu ko a gidan iyayen su iya abin da zasu samu kenan.
3. Sannan yasa mana Albashi na ₦10,000 duk wata, duk dan mu samu kwarin guiywa na yin karatun mu, kuma wadannan kudade kowa ya samu har zuwa lokacin daya sauka daga mulki.
4. Ya samar mana da na’ura mai kwkwalwa duk dan saboda kar muji mun fita daban da sauran daliban manyan attajiran da suke a wannan makaranta tamu.
5. Ya kawo mana ziyara yadda ko wane uba yake kaiwa dansa ziyara in ya kaishi makaranta a waje da gida, ya dauki hotuna dama, kusan awansa daya da rabi a tsaye saboda yawan mu, duk dan yadauki hoto da kowa daga cikin mu.
6. Ya canja wa daruruwan mutane rayuwa, dan da badan haka bad a watakila wasu daga cikin mu da tini suna shaye-shaye ko wani abu mara nagarta a cikin al’umma.
7. Ya wayarwa mana da kai ta fuskar da said a muka sake gane muhimman cin karatu.
8. Kuma yayi abin da da ace ko wane shugaba a kasar mu abunda zaiyi kenan har ya gama mulkin sa da an samu canji ba a matakin jiha bama har a matakin kasa baki daya.

WADANNAN DALILAN KADAI YASA NA ZABI JAGORAN TALAKAWA, ENG. DR RABI’U MUSA KWANKWASO. KUMA BAZAN ZAMA KAZA BA, WACCE ZATA CI TA GOGE BAKI  TA MANTA DA ABIN ALKHAIRIN DA KA MATA BA.

KWANKWASIYYA; IS AN IDEOLY FOR EVERY LEADER TO ADOPT

AHMAD BASHIR SAGAGI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button