Labarai

Dino Melaye ya shigo da wasu manyan Fastoci daga kasashen waje don su yi masa addua

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye ya shigo da wasu manyan faastoci daga kasashen waje don su yi masa addu’a akan wata matsala da bai ambata ba.

HAUSAFINEST ta ruwaito Melaye ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram, inda yace ya gayyato Fasto Shazard Sadeeque ne daga kasar Pakistan, yayin dayan faston ya taho Najeriya daga kasar Kenya, sai kuma wani Faston Najeriya, Joshua Talena Idan za’a tuna a satin data gabata ne Sanata Dino ya kai kukansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya nemi Buhari dauki mataki akan yunkurin halaka shi da wasu makiya ke kokarin yi.

Sai dai a lokuta da yawa, Dino Melaye ya sha ambaton gwamnan jaharsa ta Kogi, Yahaya Bello a matsayin mutumin dake kokarin ganin ya kashe shi, inda a kwanakin baya ya tsallake rijiya da baya lokacin da yan bindiga suka nemi kashe shi. A wani labarin kuma, wani Sanatan jam’iyyar PDP dake jahar Ribas, Osinakachukwu Ideozu ya sauka yayi wankan tsarki irin na siyasa a ranar Laraba 24 ga watan Oktoba ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inji rahoton jaridar Punch.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ahmad lawan ne ya sanar da sauyin shekar Sanata Osinakachuku a yayin zaman majalisar dattawan Najeriya na ranar Laraba. Bayan ya bayyana ma takwarorinsa na majalisa sauyin shekar Sanata, sai Ahmad Lawan ya kawo kudirin bukatar majalisar ta dage zamanta na tsawon sati biyu, sa’annan ya taya abokinsa murnar shigowa jam’iyya mai rinjaye a majalisar. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button