Labari

Dan Maina ya haru mu da bindiga yayin da mukaje damke baban sa – DSS

Dan Maina ya haru mu da bindiga yayin da mukaje damke baban sa – DSS

A ranar Larabar 2 ga watan Oktoba 2019 ne mai magana da yawun hukumar DSS, DR Peter Afunnanya ya shaida wa manema labarai cewa jami’an hukumarsa da na EFCC sun kai samame wani otal inda suka kama  tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon Najeriya wato Abdurrashid Maina.

Dr Peter ya ce a lokacin da suka je otal din sun samu Mainan ne tare da dansa mai shekara 20 wanda ya yi yunkurin far wa jami’an da wata bindigar da ke hannunsa, kafin daga bisani su ci karfinsa.

Mai magana da yawun DSS din ya kara da cewa jami’an nasu sun samu bindiga karama da alburusai da mota mai sulke kirar Range Rover da BMW da na’urar daukar hoto daga sama da kuma kudaden kasashen waje duka a tare da Abdurrashid Maina.

Hukumar DSS din ta ce za ta mika Maina tare da abubuwan da aka samu a tare da shi ga hukumar EFCC domin daukar matakin da ya kamata wajen hukunta shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button