Labaran siyasa

Dalilin raba garina da Shekarau a siyasa — Takai

Tsohon kwamishina a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a Kano, Malam Salihu Sagir Takai ya ce sun yi hannun riga da tsohon mai gidan nasa a fagen siyasa.

Malam Salihu Takai ya jima yana mu’amala da Malam Ibrahim Shekarau tun gabanin shiga siyasa a 2003, kuma yana daga cikin kwamishinonin da suka fi fada-a-ji a lokacin gwamnatin Shekarau.

Takai ne dai Shekarau ya tsayar takarar gwamnan Kano a shekara ta 2011, sannan ya sake mara masa baya a 2015.

Malam Salihu Takai ya ce ya yanke shawarar zama a PDP ne saboda dalilan da Shekarau ya bayar na fita daga jam’iyyar ba su gamsar da shi ba.

Ya ce mafi yawan mutanen da ya tuntuba gabanin yanke hukunci sun ba da shawarar ya ci gaba da zama a PDP, kada ya koma jam’iyyar APC.

A yanzu dai Malam Salihu Takai ya ce ya koma bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tun da suna jam’iyya daya.

Sai dai ya ce duk da haka babu wani sabani tsakaninsa da Malam Shekarau a mu’amala, kawai dai a siyasance ne suka raba hanya.

Tuni dai Malam Salihu Takai ya yi mubaya’a ga shugabancin riko na jam’iyyar PDP a Kano karkashin Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwakwaso ne.

A ranar Asabar da ta gabata ne tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC bayan ficewa daga PDP saboda zargin rashin adalci wajen rusa shugabancin jam’iyyar a jihar.

To sai dai PDP ta musanta zargin na Shekarau.

An fara samun sabani ne bayan komawar Sanata Rabi’u Kwankwaso PDP a watan Yuli.

A baya dai Shekarau ya shaida wa BBC cewa yana maraba da shigar Kwankwaso PDP, kuma za su yi aiki tare domin kai jam’iyyar ga nasara a jihar Kano.

To sai dai tun tafiya ba ta yi nisa ba tsofaffin gwamnonin biyu suka raba gari.

Da ma wasu masharhanta al’amuran siyasa na ganin zai yi wuya Shekarau da Kwankwaso su iya zama a jam’iyya daya, saboda mummunar hamayyar da ke tsakaninsu, da kuma banbancin ra’ayi.

Source: bbchausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button