Labaran siyasa

Dalilin dayasa kwankwaso bai nemi tazarce ba-Mahammad Garba

Dalilin da yasa tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai sake tsayawa takara ba shine tsoron shan kayi a hannun a tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, kamar yadda gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana.

Kwamishinan yada labaran gwamnan jahar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 20 ga watan Janairu, inda yace Kwankwaso ya ji tsoron kada Shekarau ya kunyatashi ne yasa bai sake neman tsayawa takarar Sanata a zaben 2019 ba.
Malam Garba ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a gangamin yakin neman zaben Ganduje daya gudana a karamar hukumar Karaye ta jahar Kano, inda ya bayyana Kwankwaso a matsayin ‘Kararre’, wanda bashi da wata sauran tasiri a siyasar Kano.

“Sanata Kwankwaso ya fahimci tabbas idan ya tsaya takara da Shekarau zai sha kunya, don haka yasa yayi yan dabaru ya janye daga tsayawa, domin ya san babu makawa sai Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya kayar da shi.

“Idan baku manta ba Shekarau ya yi ma Kwankwaso jina jina a zabukan 2003 da 2007, inda ya kayar dashi a zaben gwamna a 2003, sa’annan ya kayar da dan takararsa a yayin zaben gwamna na shekarar 2007.” Inji shi.
Bugu da kari, Garba yace irin kalaman da Kwankwaso ke furtawa a yayin kamfe ya nuna cewar bashi da masaniyar sauyin da aka samu a siyasar jahar Kano, kuma kalamai ne irin na wanda ya riga ya san ba zai ci zabe ba.

“Zaizayewar Kwankwasiyya, da kuma yadda jigoginta suke ficewa daga cikinta suna dawowa cikin jam’iyyarmu mai albarka, jam’iyyar APC ya nuna cewa mun kayar da Kwankwaso da dan takararsa na gwamna tun ma kafin a kada kuri’a.” Inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button