Labaran siyasa

Dalilin Da Ya Sa Sanatocin APC Suka Kasa Tsige Saraki -Shehu Sani

Dalilin  Da Ya Sa Sanatocin APC Suka Kasa  Tsige Saraki -Shehu Sani

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, wanda ya fice daga Jam’iyyar APC kwanan nan, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sanya takwarorinsa ‘yan Jam’iyyar ta APC suka ki su tsige Shugaban Majalisar Ta Dattawa, Bukola Saraki.

Shehu Sani, wanda yana daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar PRP a halin yanzun ya ce, sun kasa tsige Saraki ne saboda, yin hakan ya sabawa tsarin mulki. Sani wanda ya yi wannan maganan da manema labarai a Abuja, ya ce, sannan kuma ita kanta Jam’iyyar ta APC ba ta da yawan ‘yan majalisun da za ta iya yin hakan.

Shugaban Jam’iyyar ta APC ya fi kowa zakewa da yin barazanar ganin an tsige Saraki din, matukar ya ki sauka da girma da arziki. Shi kuma Saraki, ya sha alwashin ba wanda ya isa ya tsige shi tun da mafiya yawan ‘yan majalisun suna tare da shi ne.

Ko da Majalisar ta dawo daga hutun da ta tafi, sai ‘yan Jam’iyyar ta APC suka yi shiru da maganan, ba su furta uffan a kan hakan ba. “A hukunce, ba abu ne mai yiwuwa ba a tsige Saraki, saboda Jam’iyyar APC ba ta da kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar. Na biyu kuma, Saraki ya iya runguman kowa a tafi tare, yana shugabanci ne ta yadda hatta masu sukan sa ma yana yi tare da su.

Shehu Sani, wanda yake neman a sake zabensa a karkashin tutar Jam’iyyar PRP, ya ce hatta wakilan Jam’iyyar adawa ta PDP sun fi wakilan Jam’iyyar APC hadin kai a cikin Majalisar.

“Wannan shi ya sanya a tsige Saraki ta hanyar da tsarin mulki ya tanada, ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda ‘yan APC a majalisar kansu ba a hade ne yake ba.

APC ba su kuma da yawan da za su iya yin hakan.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button