Labarai

Dalilin da ya sa Kungiyar Kwadago ta janye yajin aiki

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta janye yajin aikin da ta kudiri farawa yau Talata, 6 Ga Nuwamba, domin neman karin albashi.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya bayyana haka jiya Litinin cikin dare, a Abuja bayan kammala taron bangarori uku da aka gudanar tare gwamnatin tarayya.
Kungiyoyin kwadago sun yi niyyar tafiya yajin aiki saboda gwamnatin tarayya ta kasa biya musu bukatar maida mafi kankantar albashi daga naira 18,000 zuwa naira 30,000.
Da ya ke magana da manema labarai, Wabba ya ce, “Tattaunawar da aka yi a daren yau da kwamiti, ya kammala aikin da aka dora masa. An cimma yarjejeniya, kuma kowane bangare ya sa hannu. Za a damka wannan rahoto ga Shugaba Muhamamadu Buhari ranar Talata, da karfe 4:15.
“Tunda an cimma wannan matsaya, kuma an kammala aikin da aka dora wa kwamiti, wannan ya sa muka yanke shawarar janye yajin aiki, ko kuma muka jingine yajin aiki a yanzu tukunna.”
Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya jinjina wa kwamitin sakamakon yadda suka sadaukar da lokacin su wajen zaman cimma yarjejeniyar da aka yi.
Ita ma shugabar kwamitin, Amma Pepple ta tabbatar da cewa yau Talata za a kai wa Shugaba Buhari rahoton kwamitin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button