Labarai

Dalilin da ya sa ba za mu iya binciken Ganduje ba -EFCC

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ba za ta iya binciken Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ba, saboda ya na da kariya ta dokar kasa, wacce ba ta yarda a binciki gwamna ko a tuhume shi ba har sai ya sauka daga mulki.
Haka EFCC ta buga a shafin ta na twitter jiya Alhamis, a matsayin amsa daga wata kungiyar bin diddigi da hana almundahana, mai suna ‘Tap Nitiative for Citizen Development.
Wannan ne karo na uku da ake yi wa EFCC tambaya a kan bidiyon wawuran kudaden da aka nuno Ganduje ya yi, wanda ya jawo ka-ce-na-ce da alamar tambaya a kan sahihancin yaki da cin hanci da gwamnatin Buhari ke yi.
Tsakanin 11 Ga Oktoba zuwa yanzu dai an saki bidiyo shida wadanda aka nuno Ganduje na karbar dalolin da aka ce sun kai milyan biyar.
Nitiative ta sake yi wa EFCC tambayar cewa to idan EFCC din ba za ta iya binciken Ganduje ba saboda ya na rigar kariyar bincike daga doka, don me ya sa ta binciki gwamna Fayose a lokacin da shi ma ya ke gwamna?
A nan ne EFCC ta sake maida amsa da cewa ba ta fitowa waje ta na fallasa wasu bayanai na ta na sirri.
Daily Nigerian wadda ta fallasa Ganduje a baya ta ruwaito cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a bincike badakalar Ganduje, amma har yau shiru.
Buhari dai ya yaba wa salon mulkin Ganduje a wani taron da ya yi da ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa cikin makonni biyu da suka gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button