Labarai

Dalilanmu na sayar da kayan gwanjo na mata musamman underwears

– Wata mata mai saida Gwanjo tanajin dadin yanda mata ke tururuwa wajen siyan kayanta

– Mata da dama sunfi son kayan gwanjon akan sabo – Wani likita yace za’a iya samun kwayoyin cuta a kayan gwanjon inda ba’a tsabtace su yanda ya kamata ba Wata mata wadda ke sana’ar saida kayan gwanjo a Umuahia dake Abia ta bayyanawa NAN yanda takejin dadin sana’ar ta. Matar ta bayyana yanda mutane ke tururuwa wajen siyan kayan nata wanda suke kira da “Okrika”. Daya daga cikin masu siyan irin kayan tace ita da wasu mata da dama sunfi jin dadin siyan kayan gwanjon sama da sababbi. Ta kara da cewa bawai tana siyan kayan bane don suna da sauki tana siya ne saboda sunfi sabbabi karko. NAN ta tattauna da wani mutum dayazo wucewa donjin ra’ayin sa akan irin wadannan kaya inda yake cewa 

“bawai wanduna kadai matan ke siya ba kullum Idan na wuce ina ganin yanda sukeyin dandazo wajen diban kayan.” “Wannan kadai ya isa ya nuna maka karancin tattalin arzikin da kasarmu take fama dashi,Nageriya ta bada kanta ta hanyar amincewa da shigo mata da kowanne irin kaya daga America, Europe, Asia da kuma sauran kasashe. Wani likita dake aiki a gidan gwamnatin Abia yace za’a iya samun kwayoyin cuta a cikin kayan gwanjon matukar ba’a tsabtacesu yanda ya kamata ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button