Labaran siyasa

Dalilan da suka sanya na koma jam’iyyar PRP – Takai

Malam Salihu Sagir Takai ya bayyana dalilan da suka sanya ya fice daga cikin jam’iyyar PDP zuwa sabuwar jam’iyyarsa ta PRP da ya yanki katin shigarta a ranar Alhamis.
Takai ya bayyana cewar rashin adalcin da aka yi musu a PDP bayan sun cika dukkan ka’ida da dokokin shiga zabe amma aka tauye musu hakki.
”A bisa doka da ka’idar jam’iyya dole a sanar da dan takara awa 48 kafin yin zaben fidda gwani na jam’iyya sannan a bashi sunayen wakilan da zasu gudanar da zabe, amma babu ko daya da aka yi, kawai muka ji labarin wai anyi zaben fidda gwani na PDP a gidan wani mutum”
”Mun rubuta korafi tare da kokenmu ya uwar jam’iyyar PDP ta kasa akan a bi mana hakkinmu bayan mun bi dukkan ka’idoji, amma uwar jam’iyya ta gaza yi mana adalci a wannan halin “
”A sabida haka muka yanke shawarar sallama jam’iyyar PDP dan haka muka nutsu tare da gamsuwa da jam’iyyar PRP kuma muna fatan Allah ya bamu Nasara” A cewar Malam Salihu Sagir Takai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button