Labaran siyasa

Da Dumi-Dumi: Gwamna Rochas Okorocha ya Fice daga Jam’iyyar APC Yace ba Jam’iyya ce ta Mutane Nagari ba.

Governor Rochas okorocha
Labaran dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani na nuni da cewa gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Inda aka bayyana cewa gwamna Owelle Rochas Okorocha ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar sa ta APC zuwa jam’iyyar AA domin ya hadu da sirikin sa Uche Nwosu.
A cewar su Rochas ya bayyana ficewar sa ne  a yayin bukukuwan Kirsimeti daya gudana a fadar gwamnantin jihar Imo.
Rochas yace “Na sani Al’ummar jihar Imo baza su taba goyon bayan wadanda suka sace masu tikitin takarar gwamnan su da suke so a zaben 2019 ba”
“Sun tsaya a gefe daya suna jiran wanda zasu zarga game da rashin kyautatawar da suka aikawa jama’ar jihar Imo”
 “Sun san gaskiya cewa al’ummar jihar Imo ba za su goyi bayan duk abinda aka ce satar sa akayi  ba, wannan shine dalilin da yada jama’ar Imo suka yi magananin ‘yan 419 a shekarar 1997.
Rochas ya kara da cewa “wadanda suka fito da wannan labarin cewa na fice daga jam’iyya ta APC zuwa jam’iyyar AA,  damuwa ce tasa su yada labaran wanda kuma ba gaskiya bane”
“Matsalar da suke fuskanta na samun haramtaccen tikitin takara, shine ya sanya suke jin dacin goro a bakin su wanda ba shine asalin dandanon sa ba”
“Suna anfani da maganganun bata mana suna, anma babban kalubalen su yanzu shine yadda za su gamsar da jama’ar Imo su zabe su a 2019.

“Daga cikin batancin su gare mu shine, a garin Abuja sun gayawa magoya bayan su cewa za suci zabe ko babu Rochas Okorocha, idan abinda suke fadi gaskiya ne  me yasa har yanzu suke damuwa akan Rochas da kuma harkokin siyasar sa”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button