Labaran wasanni

Conte Ya Na Tattauna Wa Da AC Millan

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta AC Millan ta fara shirye shiryen korar mai koyar da ‘yan wasan kungiyar wato Gannaro Gattuso domin daukar Antonio Conte. 


AC Millan dai ta amince zata biya Conte fam miliyan 10 domin ya zama mai koyar da ‘yan wasan kungiyar sai dai wasu rahotannin sun bayyana cewa shugaban kungiyar, Leonardo ya bayyana cewa baza su kori Gattuso ba a wannan lokacin. 

A kakar wasan data gabata Gattuso dai ya lashe wasanni 16 cikin wasanni 36 daya jagoranci kungiyar wanda hakan yasa ake ganin hakan baiyi kokari ba kuma yakamata kungiyar ta canja shi. 

Conte ya bar Chelsea bayan da kungiyar ta koreshi inda ta maye gurbinsa da Mauricio Sarri, shima dan kasar Italiya duk da cewa Conte ya lashe kofin Firimiya da kuma gasar cin kofin kalubake ta FA cikin shekaru biyu a kungiyar. 

A kwanakin baya an ruwaito cewa Conte yana shirin kai kungiyar Chelsea Kotu, bayan dayayi zargin cewa kungiyar ta cuceshi saboda bata koreshi da wuri ba gashi har lokaci ya kure wajen neman sabuwar kungiya. 

Gattuso dai yakai AC Millan matsayi na shida a kakar wasan data gabata kuma ya buga gasar cin kofin Europa da kungiyar ta AC Millan sai dai kasancewa Conte Bashi da kungiya zaisa kungiyar ta koreshi. 

Conte dai yanada kwarewa a gasar siriya A bayan ya lashe kofin na siriya A guda uku da kuma kofin kalubale guda uku da kungiyar Jubentus acikin shekaru uku da yayi da kungiyar kafin kuma ya koma ya karbi tawagar kasar Italiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button