Labari

BURINA A KULLUM NA GA NA TALLAFAWA RAYUWAR MATA DA MATASA

BURINA A KULLUM NA GA NA TALLAFAWA RAYUWAR MATA DA MATASA- HAJIYA BALARABA GANDUJE

Hajiya Balaraba kenan yayin wani bada tallafi

Diyar mai girma gwamnan jihar kano Haj. Balaraba Abdullahi UMAR Ganduje ta bayyana cewa ita a rayuwar ta tanaso taga ta taimaki matasa maza da mata gajiyyayu
Da take bayyana hakan a shafinta na Facebook ta bayyana:

Ni Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, Babban burina a kullum shi ne na ga na tallafawa rayuwar ƴan uwana MATA da kuma MATASA ta fannonin rayuwa daban-daban waɗanda za su zama sanadiyyar kyautata rayuwa da kuma walwalarsu.

Sanin kowa ne yau MATA da MATASA su na cikin fuskantar tarin matsaloli ta fuskar karatu da kuma sana’o’in dogaro da kai gami da amfanar mulkin dimokaraɗiyya yadda ya kamata.

Duk kuwa da cewar MATA su ne tubalin ginin tarbiyya da kuma samar da al’umma nagari a rayuwa gaba ɗaya. Idan aka tallafawa MACE ɗaya, tamkar al’umma gaba ɗaya aka taimakawa

MATASA kuwa su ne ƙashin bayan cigaban al’umma da kuma kyautata zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi. Idan aka tallafa musu su ka tsaya da ƙafafunsu tamkar tubalin ginin ɗorewar zaman lafiya da cigaban ƙasa aka gina.

Da ikon Allah kamar yadda na faro, ba zan gajiya ba wajen ganin na cigaba da taimakawa rayuwar MATA da MATASA da kuma gajiyayyu da mabuƙata ba har abada.

Ina fatan za ku cigaba da sanya ni cikin addu’o’inku Allah ya ƙarfafe ni kan wannan aniya tawa ta alkhairai.

TO MUMA MUNA ADDUAR ALLAH YA CI GABA DA BAKIN IKON AIWATAR DA WANNAN ALHERI YA KAREKI DAGA SHARIN MASU SHARRI AMEEN

Domin Samun Sababbin Labarai kasance da www. Hausafinest.com.ng domin kawo muku labarai cikin harshen Hausa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button