Labaran wasanni

Budurwar Ronaldo Ta Goyi Bayan Sa

Budurwar zakaran dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo, Goergiana Rodriguez, ta wallafa sakonta na goyon baya duk da zargin da ake masa na yiwa wata fyade a birnin Las Vegas, da ke Amurka.

Kathryn Mayorga, tana zargin shahararran dan wasan Juventus, da yunkurin yin lalata da ita ba tare da amincewar ta ba a cikin dakin Otel dinsa a shekarar dubu biyu da tara.

Lauyoyin dan wasan sun musanta wadannan zarge-zarge da ake yi a kansa. Yanzu mayorga, ta shigar da kara akan tsohon dan wasan kungiyar Manchester United. A wani sakon Instagram da Ronaldo ya tura ya nesanta kansa da zarge-zargen da ake masa inda yay a ce labaran karya ne kawai.

Kuma yanzu abokiyar zamansa ta bayyana cikakkaen goyon bayyanta, tare da tura sako ta shafinta na Instagram, na nuna soyayya. Rodriguez ta rubuta cewa “Ko yaushe kana kokarin ka canza matsalolin dake tunkararka domin nuna cikakken kwazon da kake dashi”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button