Labarai

BIKIN SAMUN NASARA:AN FARA BIKIN MURNAR SAMUN NASARAR GWAMNA GANDUJE A KOTU

AN FARA BIKIN MURNAR SAMUN NASARAR GWAMNA GANDUJE A KOTU

Yanzu haka a sassa daban-daban na birnin Kano ɗumbin al’umma masoya mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun fito kan tituna wasu a ƙafa wasu cikin motoci da sauran ababen hawa ɗauke da waƙoƙin mai girma gwamna su na shagalin murnar samun nasarar gwamna Ganduje a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna.

Kotu dai ta yi fatali da dukkan shaidun da Kwankwasiyya su ka gabatar mata,
Ta yadda hakan ke nuni da cigaba da zaman gwamna Ganduje daram kan kujerar gwamnan Jihar Kano, ya yin da shi kuma Abba zai koma ya cigaba da zaman gida.

Ɗumbin matasa dai sun yi dandazo ɗauke da waƙoƙin gwamna Ganduje su na farin ciki da murnar wannan nasara.

Ku cigaba da kasancewa da HAUSAFINEST NEWS zam cigaba da gabatar muku bayanai kan halin da ake ciki a wannan rana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button