Kannywood

Biki buduri: Ado Gwanja zai angwance, ya fitar da ranar daurin auren sa

Mawakin wanda aka yi ma lakabin ‘limamin mata’ zai angwance ga amaryar shi ranar 12 ga watan Oktoba.

Ranar da aka dade ana jira ta bayyana inda mawaki kuma jarumi mai tauraro, Ado Isa Gwanja, ya sanar da ranar daurin auren sa.

Tun da dadewa masoya da masu bibiyan jarumin suke neman amsar tambayar ranar da za’a daura auren shi da masoyiýra shi wacce ta sace zuciyar wanda daga bisani baya boye nuna kaunar da yake mata a shafin sa na kafafen sada zumunta.

Mawakin zai angwance ga amaryar shi, Maimunat Kabir Hassan Danauta, cikin wannan wata.

Za’a daura auren su ranar 12 ga watan Oktoba a jihar Kano dai dai karfe hudu na yamma.

Jarumin wanda ake ma lakabi da ‘Limamin mata’ ya wallafa katin gayyata na auren shi a shafin sa. Hakan ya biyo bayan hotunan kafin-aure da ya fitar.

Hotunan sun mamaye shafuka da dama inda sauran abokan sana’ar sa ke masa fatan zaman lafiya a auren shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button