Kannywood

Biki bidiri burede: ‘Dan wasan Kannywood Booth ya samu kyakkyawar matar aure

An sa ranar auren Tauraron ‘Dan wasa kuma mai shirya fim din Hausa

– Ana sa rai dai Ramadan Booth zai shiga daga ciki a karshen watan Yuni

– Furodusan da Mahaifiyar sa da ‘Yanuwan sa duk fitattu ne a harkar fim

Labari ya zo mana daga kafafen yada labaran cikin gida cewa Babban Dan wasan Hausa dinnan watau Ramadan Booth zai zama Ango cikin ‘yan kwanakin nan.

Kwanan nan ne aka fitar da wasu hotuna na Jarumin tare da Amaryar ta sa. Rade-dadi ya fara yawo cewa za ayi daurin auren ne a karshen wannan wata. Idan ta tabbata a Ranar Asabar 30 ga wannan wata za a sha biki.

Tuni dai jama’a su ka fara tofa albarkacin bakin su bayan ganin hotunan fitaccen ‘Dan wasan kuma mai shirya fim da tsaleliyar sahibar sa mai ‘dan karen kyau. Da dama dai daga cikin ‘Yan dangin su ba baki bane a fim.

Kwanakin baya ma Ramadan Booth yayi wani fim inda a ciki yayi soyayya da ‘yar uwar sa wnda ita ma fitacciyar jaruma ce watau Maryam Booth. Mahafiyar su Zainab Booth ma tayi fice a harkar wasan kwaikwayo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button