Kannywood

Bidiyon tsiraici ya bayyana da ake zargin jarumar film Maryam Booth ce a ciki

Gajeren bidiyon wanda baifi dakika uku ba, an danganta shi da wani Sanatan arewa, da sunan cewa shine a cikin bidiyon duk kuwa da cewa daga nesa akayi daukar ba kuma yadda za ayi a iya tabbatar da hakinan tabbacin cewa shi dinne.
Sai dai bidiyon ya cigaba da zaga yawa a shafin na Twitter inda har ya ketara zuwa shafin Facebook, inda wasu ke ikirarin cin mutuncin siyasa ne kawai ake so a yiwa Sanatan, wasu kuma na cewa shi dinne, wasu kuwa na Allah wadai da masu yada tsiraici, domin koma waye bai kamata a sanya shi ba, domin kuwa haramun ne yada alfasha.
Ana tsaka da haka kuma a yau sai wani bidiyon ya sake bayyana shima dai mai tsawon dakika uku mai dauke da wata budurwa a tsaye ita ma tsirara haihuwar uwarta, tana rike da dan kamfe tana shirin sanyawa a bakin gado mai daukar kuma yana daga kan gado, ganin cewar ana daukarta yasa tayi sauri ta zo ta kwace abin daukar.
To ita ma dai wannan budurwa sun ce jarumar fina-finan Kannywood ce wato Maryam Booth, amma sun fadi hakan ne saboda ta zo har kusa dame daukar bidiyon, inda aka gano kamanceceniya da za a iya gani tsakanin ta da wacce ake dangantawa a bidiyon wato Maryam Booth.
Ba za mu iya sanya muku wannan bidiyon ba kasancewar ya saba ka’idojin addini, al’ada da kuma shafinmu, amma zaku iya cigaba da kasancewa tare damu domin jin yadda za ta kaya akan wannan rikita-rikitar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button