Kannywood

Bidiyon tsiraici: Jaruma Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamariFitaciyyar jarumar nan ta masana’antar  Kannywood, Maryam Booth ta yi martani a kan bidiyon tsaraicinta da ke yawo a shafukan sadarwa.

A ranar Juma’a ne  sai wasu kafafen soshiyal midiya su ka ambaci Deezell a matsayin wanda ya saki bidiyon domin ya tozarta ta bayan soyayyar su ta rushe.

Nan da nan Deezell ya karyata zargin a wata sanarwa da ya bayar a Twitter da Instagram. 

To amma Maryam booth ta karyata shi a cikin daren Juma’a, ta ce ba shakka shi ne ya dauki bidiyon ta a lokacin da ta ke kokarin saka kaya.

A cikin sanarwar da ta bayar a karon farko kan wannan badakala, wadda ta saka a shafukan ta na soshiyal midiya, Maryam Booth ta ce: 

“Ina sane da abubuwan da ke wanzuwa yanzu da kuma surutan da ake yi a kafafen yada labarai ga me da wani bidiyo da aka ce ni ce, aka yaɗa a kafofi da dama na soshiyal midiya, kuma dubban mutane su ka kalla. 

Da farko, na yi niyyar in yi shiru har sai jami’an tsaro sun kammala nazarin su da binciken su. 
“Maganar da wani mutum mai suna Ibrahim Ahmad Rufa’i, wanda aka fi sani da sunan Deezell, ya yi, ita ta saka ni tilas in ce wani abu.

 “A matsayi na na ‘ya mace, ‘yar wasa kuma wadda wasu ke kwaikwayo da ita, ba zan bari a shashantar da wannan maganar ba. 

“A gaskiya, ina so in bayyana cewa shi wannan mutum (Ibrahim Ahmad Rufa’i) ya sha yi mani barazanar cewa zai saki bidiyon idan ban ba shi kudi ba. 

“A matsayi na na ‘ya mace, jarumar fim kuma wadda miliyoyin mutane ke koyi da ita, na yi ta kokarin na kare mutunci na ta kowace hanya da zan iya, amma kawai ba tare da sani na ba sai wannan bidiyo da ya shekara uku da ɗauka ya ɓullo.

 “A yanayi irin wannan, tilas mutum ya tsaya ya yi karatun ta-nutsu kafin ya ce komai, amma gaskiya ne cewa Deezell tsohon saurayi na ne wanda kuma shi ne ya dauki hoton bidiyo na a lokacin da na ke saka kaya. 


“A yanzu ina ta faman tuntubar abokan shawara ta don samun hanyar daukar matakin shari’a da ya dace kan dukkan wanda ke da hannu cikin al’amarin sakin wannan bidiyo. 

“Ina godiya ga iyaye na da ‘yan’uwa na da kawaye na da abokai na, da kuma musamman masoya na, saboda yadda su ka nuna tausayawa a gare ne a wannan mawuyacin hali. Na gode maku baki daya.” 


Source: legit/twitter

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button