Labaran Duniya

BAYYANAR BIDIYON BABA NA GWAGGO MAI DALOLI

*Zuwa Ga BABA BUHARI DA EFCC

Daga Nasiru Salisu Zango

Batun wannan fefen bidiyo zai bude wani sabon shafi a siyasar birnin mahangur6a, domin hatta yadda manya suka wawashe shagunan kasuwar kantin tudu aka bar talakawa na kuka a gidajen rediyo, ya fito sosai a kunshin wancan bidiyo kai hatta, ‘yan majalisar kashe muraba ma,an jiyo Oga yana cewar a baiwa ‘yan gaba gaba daga cikinsu shago da naira miliyan 5,domin suma su lasa su kuma ja bakinsu suyi gum.

Kai jama’a ! Wannan badali fa ana yinsa ne akan kasuwar da akace za a gyara domin talaka ya sabun ta, ashe-ashe wayon aci ne an kori kare daga gindin dinya.

Duk da cewar wannan batu nawa duka ne a murde, amma dai idan kaji makaho yace azo ayi wasan jifa to dutse ya taka. Ni dai babban takaici na shine yadda ake cigaba da rayuwar kashin dankali a birnin Mahangur6a, shi kuwa kashin dankali ba abu ne mai kyau ba domin murgujeje ne yake danne dan mitsili.

Yanzu haka dai kallo ya koma sama wai shaho ya dauki giwa, domin kuwa su talakawan birnin sune zasu yiwa kansu alkalanci domin yanzu ne dama take a hannun su, kodai su zabi cigaba da zama a hannun Baba na gwaggo mai Dala daloli, wanda a yanzu ya sami lambar girma ta sahibul fulus waddalal Amurkiyya, ko kuma su sauya lale, dama hannun su ne ya zabo musu.

Ni dai nasan bana farin ciki dan wani ya afka cikin jarraba ko masifa amma na kan yi jawabi idan hadama ko cinzali suka sa ido ya raina fata ko ba komai ya zama izina ga na baya.

“Maa asabaka min hasanatin fa minallah wama asabaka min sayyi’atin famin nafsik…”
Alaramma idan nayi kure a gyara min.

Allah Ya sa muyi kyakyawan karshe, na Annabi yace Amin…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button