Labaran wasanni

Barcelona Ta Sa Dembele A KasuwaRahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana shirin siyar da dan wasanta Ousmane Dembele wanda yakoma kungiyar daga Borussia Dortmund a kakar wasan data gabata. 

Barcelona ta biya kusan fam miliayn 100 wajen siyan dan wasan mai shekara 21 a duniya wanda yafara buga wasansa tun yana matashi da kungiyar kwallon kafa ta Rennes dake kasar ta Faransa. Dan wasan ya wakilci kasarsa ta Faransa a gasar cin kofin duniyar da suka lashe a watan daya gabata sai dai bai fito ba a wasan karshen da suka doke kasar Crotia daci 4-2 a kasar ta Rasha. 
Kamar yadda rahotanni suka bayyana kungiyar tana tunanin ko za ta siyar da dan wasan a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa a wata mai zuwa bayan da ake tunanin kungiyar za ta bukaci fam miliyan 71 ga duk kungiyar da take son siyansa.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ce ta kasar Faransa take zawarcin dan wasan domin yakoma ya buga mata wasa yayin da ita ma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta nemi dan wasan a kwanakin baya.

Dembele ya bugawa Barcelona wasanni 27 ne gaba daya tun bayan komawarsa kungiyar sannan kuma ya zura kwallaye hudu a raga sai dai yasha fama da ciwo tun farkon komawarsa kungiyar inda yayi jinyar watanni hudu a farkon kakar data gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button